Yadda Naja’atu ta bi Tinubu har kasar Waje Saboda Kwadayin Kujerar Kamfe Inji Minista

Yadda Naja’atu ta bi Tinubu har kasar Waje Saboda Kwadayin Kujerar Kamfe Inji Minista

  • Festus Keyamo ya ce abin da Naja’atu Mohammed ta fada a game da Bola Tinubu ba gaskiya ba ne
  • ‘Yar siyasar tayi zama da ‘dan takaran shugaban kasar a Landan, ta fito tana cewa bai da koshin lafiya
  • Kakakin kwamitin APC-PCC ya ce saboda a ba ta Darektar kamfe Naja’atu ta zauna da Tinubu

Abuja - Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo ya zanta da Punch, ya tabo jerin ikirarin da Naja’atu Mohammed ta ke yi.

A hirar da aka yi da shi Festus Keyamo ya karyata Naja’atu Mohammed, yake cewa tun farko an gano ‘yar siyasar zagon kasa take yi wa Bola Tinubu.

Ministan yake cewa kafin ‘yar siyasar ta fara sakin kalamai, an fada mata ta bar kwamitin yakin zaben domin an gano take-taken da take da shi.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ankarar da Magoya-Baya a Kan Sirrin Jawo Wahalar Fetur da Karancin Nairori

Keyamo yake cewa Naja’atu Mohammed ta tashi har zuwa Landan ta zauna da Bola Tinubu ne saboda ta samu kujerar Darekta a kwamitin kamfen APC.

Yan APC
Yakin zaben APC Hoto: @OfficialAsiwajuBAT
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Festus Keyamo

“Ta yi ta bin Asiwaju (Bola Tinubu) har Landan domin ta lallabe shi a ba ta mukamin nan. Amma an yi ta sa mata idanu ne kurum.
An san cewa zagon-kasa ta zo tayi wa tafiyar jam’iyyar APC. Da ta je Landan ta ga Tinubu yana da matsala, meyasa ta karbi aikin?

Meyasa ta dawo Najeriya, ta jira na tsawon watanni hudu kafin ta ajiye kujerar da aka ba ta.
Kwadayin mukami ya jawo ta tafi Landan. Masu daraja ba za su rika yawo kasashen Duniya su na bin Asiwaju (Bola Tinubu) ba?
Meya hana ta (Naja’atu Mohammed) haduwa da shi (Bola Tinubu) a Najeriya, meyasa za ta bi shi Landan?

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

- Festus Keyamo

Tinubu zai lashe zaben 2023

A tattaunawar da ya yi da jaridar, Kakakin kwamitin yakin neman zaben na Bola Tinubu ya ce zargin ba a iya ganin Bola Tinubu, sam ba gaskiya ba ne.

Keyamo ya ce kullum ‘dan takaransu yana zama da jama’a, yana yawon kamfe, ya kara da cewa tikitin Musulmi-Musulmi ba zai hana APC kai labari ba.

Matsayar Dattawan Arewa

Rahoto ya zo cewa Kungiyar Dattawan Arewa ta NEC ya bukaci Muhammadu Buhari Buhari ya yi hattara, na-kusa da shi da ke neman jawo hatsaniya a zabe.

Kungiyar ta ce ta na tare da duk abin da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin da NEF ta ce ba za ta maidawa Gwamna Nasir El-Rufai raddi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng