Machina da Lawan: Kotun Koli ta Yanke Hukunci kan Halastaccen 'Dan Takara Yobe ta ta Arewa

Machina da Lawan: Kotun Koli ta Yanke Hukunci kan Halastaccen 'Dan Takara Yobe ta ta Arewa

  • Sanata Ahmad Lawan ya lallasa Bashir Machina a gaban kotun koli ta Najeriya kan shari'ar takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa a APC
  • Hukunci mafi rinjaye ya jaddada cewa, Lawan shi ne halastaccen 'dan takarar kujerar sanatan APC na Yobe na Arewa
  • Amma hukunci mara rinjaye ya bayyana cewa Machina ne mai nasara kuma APc ta biya shi diyyar N3 miliyan saboda Machina bai yi zaben fidda gwani ba

FCT, Abuja - Kotun koli ta tabbatar da Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya matsayin 'dan takarar sanata na yankin Yobe ta arewa a karkashin jam'iyyar APc a zabe mai zuwa, jaridar TheCable ta rahoto.

Machina da Lawan
Machina da Lawan: Kotun Koli ta Yanke Hukunci kan Halastaccen 'Dan Takara Yobe ta ta Arewa. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

A hukunci mafi rinjaye da aka yanke a ranar Litinin, kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka kara wacce ta ayyana Bashir Machina matsayin 'dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa a APC.

Kara karanta wannan

Yobe Ta Arewa: Kotun Allah Ya Isa Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Shari’ar Lawan Da Machina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A hukuncin, Mai shari'a Centus Nweze ya soki yadda Machina ya bi ya kai karar gwaban babbar kotun tarayya da ke Damaturu ba tare da shaidar baka ba wurin tabbatar da zargin damfara.

A hukunci mafi rinjaye, kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka kara ta shiyyar Gome wacce ta jaddada hukuncin kotun kasa wacce tace Machina ne 'dan takarar Sanatan Yobe na Arewa a APC, Channels TV ta rahoto.

Amma yayin rarrabe hukuncin, Masu shari'a Emmanuel Agimo da Adamu Jauro, sun ce Ahmada Lawan bai yi zaben fidda gwani da na jam'iyyar APC da aka yi ranar 28 ga watan Mayu kuma da kanshi ya janye domin yin zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka ranar 8 ga Yunin 2022.

Hukuncin maras rinjaye ya bayyana cewa, yin wani zaben fidda gwanin a ranar 9 ga Yunin 2022 wanda Lawan yayi nasara, yayi karantsaye ga sashi na 84, sakin layi na 5 na dokokin zabe saboda APC ba ta soke zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 28 ga watan Mayu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

Mai shari'a Centus Nweze da ya karanto hukuncin, yace hukuncin babbar kotun tarayya a Yobe da ta kotun daukaka karar dole ne a ajiye su gefe.

Sai dai, alkalan biyu sun ki amincewa da hukuncin kotun koli mafi rinjaye.

A hukuncinsu da Mai shari;a Jauro ya karanto, hukuncin kotun daukaka kara yayi daidai. Ya bukaci APC ta biya Machina diyyar N2 miliyan.

'Yan daba sun kaiwa matar gwamna farmaki

A wani labari na daban, wasu bata-gari sun kai wa Lami Ahmadu Fintiri farmaki kan hanyarta ta zuwa Mubi.

Duk da bata samu rauni ba, sun fasa kan mutum daya cikin tawagarta yana samun sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel