Gwamna Ganduje Ya Fito da Abin da yake Cikinsa, Ya Tona Dalilin Canza Kudi
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana a kan canza takardun kudi da bankin CBN ya yi
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya da mugun nufi a kan APC
- Gwamnan Jihar Kano yana ganin Godwin Emefiele ya kawo tsarin ne saboda ya rasa samun takara
Abuja - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya zargi Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da canza kudi saboda ya gagara samun tikiti.
Da ya zanta da BBC Hausa bayan Gwamnoni sun hadu da shugaban kasa, Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Gwamnan CBN da mugun nufi.
A ranar Juma’a, Gwamnan na Kano ya ce Mista Godwin Emefiele bai so a shirya zabe a Najeriya, ya kuma ce sun koka da wahalar da canjin kudin ya jawo.
Gwamnan yake cewa tsarin da babban bankin CBN ya fito da shi na canza manyan takardun kudi ya yi hannun riga da ra’ayin jam’iyyar APC da ke mulki.
Haushin rasa takara ne?
Dr. Ganduje yana zargin bita-da-kulli ne Gwamnan bankin yake yi saboda Bola Tinubu ya doke shi a zaben tsaida gwanin ‘dan takaran shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da irinsu Ganduje suke yi wa Emefiele shi ne yana kokarin damkawa 'yan adawa nasara. Zargin da har yanzu shi Gwamnan bankin bai tanka ba.
Ana zargin Godwin Emefiele ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC bayan an saya masa tikiti, amma a karshe Bola Tinubu ya yi nasara.
“Wannan ba ajandar APC ba ce, ajanda ce ta wadanda suka zagaye Shugaban Kasa, da kuma shi Gwamnan CBN wanda ya so neman ya zama Shugaban Kasa amma abin ya lalace.
“Shi ya sa suke son ko dai kar zaben nan ya gudana, ko kuma wata jam’iyyar ta lashe shi.”
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Jaridar Aminiya ta ce da aka tambayi Gwamnan game da matsayarsu a kan wannan manufa da ya samu amincewar shugaban kasa, sai ya nuna sam ba su tare.
Abdullahi Ganduje wanda zai bar mulki a Mayu yake cewa sun yi hannun riga da wannan tsari da ake zargin wasu na kusa da shugaban kasa suka fito da shi.
Kamar yadda Sahara Reporters ta fitar da rahoton, kusan wannan shi ne ra’ayin irinsu Gwamnan Kaduna da suke zargin akwai zagon-kasa cikin tsarin.
Babatun Tinubu a Ekiti
A yammacin Juma’a, labari ya zo cewa an je kamfe, sai Bola Tinubu ya bude baki ya sake yin jawabin da ke nuna suka ga Gwamnatin Muhammadu Buhari.
Tinubu yake cewa ana boye Naira ne saboda a fusata mutane har suyi fada, a jawo hatsaniya saboda a daga zabe domin a kafa gwamnatin rikon kwarya.
Asali: Legit.ng