An Ji Wani Babba a Jam’iyya Yana Shirin Karya PDP a 2023, Ya Bi Jam’iyyar NNPP

An Ji Wani Babba a Jam’iyya Yana Shirin Karya PDP a 2023, Ya Bi Jam’iyyar NNPP

  • Wasu ‘Ya ‘yan PDP a yankin Warri da ke jihar Delta su na kauracewa jam’iyyar a zabe mai zuwa
  • Irinsu Victor Umukoro sun gaji da yadda ake tafiya a PDP, sun ce za su batawa Jam’iyyar lissafi
  • Shugaban DESOPADEC a garin Warri, Magege Matthew ya za su goyi bayan Omatseye Nesiama

Delta - Hon. Victor Umukoro wanda yana cikin ‘ya ‘yan da jam’iyyar PDP take ji da su a garin Warri, ya nuna zai yi zagon-kasa ne a zabe mai zuwa.

Tribune ta rahoto Hon. Victor Umukoro yana mai cewa wasu wanda aka fusata a PDP za su ruguza jam’iyyar hamayyar kasar, sai su dawo su gyara ta.

‘Dan siyasar ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis a wajen taron da ‘dan takaran Sanatan Kudancin Delta a NNPP, Omatseye Nesiama ya shirya.

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Yi Maganar Yiwuwar Hadewar NNPP da Atiku

Victor Umukoro ya nuna zai goyi bayan takarar Commodore Omatseye Nesiama (mai ritaya).

Dole ne a fara karya PDP tukuna - Umukoro

Dalilin da ‘dan siyasar ya bada shi ne ana siyasar kazanta PDP a Warri, saboda haka za su ga bayan jam’iyyar ta su, kafin su dawo su gyara ta a nan gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce ‘dan siyasar ya taba yin takarar shugaban karamar hukumar Warri ta Kudu a PDP. A yau ana sa shi cikin manyan 'yan siyasar kauyensu.

Jam’iyyar NNPP
Magoya bayan NNPP a Warri Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A zabe mai zuwa, Hon. Umukoro ya ce lokaci ya yi da mutane irinsu Commodore Nesiama za su wakilci yankin Warri a majalisar dattawan Najeriya.

“Ni ‘dan jam’iyyar PDP ne, amma abin da nake fada shi ne ‘abin ya isa haka nan’. Za mu karya PDP dinnan, mu dawo mu gyara ta.

Kara karanta wannan

Abubuwa Sun Lafa, APC Ta Fadi Wadanda Suka Kai wa Tawagar Buhari Hari a Kano

Za su fada maka cewa: ‘Ai Ran ka ya dade ya gama magana. Tsarin da za a bi kenan. Mu mun gaji, za mu kawo karshen wannan.
A zabe mai zuwan nan, ni yanzu ba ‘dan jam’iyya ba ne. Na tashi na koma ‘dan kallo.”

- Victor Umukoro

DESOPADEC za ta rungumi NNPP?

Daily Post ta ce shugaban kungiyar (DESOPADEC) ta ma’aikatan harkar mai, Magege Matthew ya ce su ma sun gaji da kamun ludayin jam’iyyar PDP.

A zabe mai zuwa, Magege Matthew ya dauki alwashin ba za su zabi ‘yan takaran PDP ba, yake cewa kuri’arsu a zaben Sanata ta na wajen Nesiama.

Kul aka zabi Atiku - APC PCC

A rahoton da aka fitar ba da dadewa ba, an ji kwamitin neman takarar Bola Tinubu a jam’iyyar APC ya nuna irin hadarin manufar Atiku Abubakar a PDP.

Asiwaju Bola Tinubu yana ganin bude iyakoki zai sa a koma zamanin shigo da abinci da makamai, amma ‘dan takaran PDP ya ce hakan zai bunkasa tattali.

Kara karanta wannan

Miyagu Sun Sace Darektan Yakin Neman Zaben Jam’iyyar APC a Wajen Yawon Kamfe

Asali: Legit.ng

Online view pixel