Bola Tinubu Ya Fadawa Manoma Katon Kuskuren da Za Ayi Idan Aka Zabi Atiku

Bola Tinubu Ya Fadawa Manoma Katon Kuskuren da Za Ayi Idan Aka Zabi Atiku

  • Bangaren harkar gona na Kwamitin neman takarar jam’iyyar APC sun zauna zauna da manoma
  • Shugaban sashen kwamitin zaben, Abubakar U. Bello ya ce akwai masu yin kamfe da bude iyakoki
  • Idan aka bude iyakokin kasar nan, kwamitin ya ja-kunnen manoma cewa komai zai dawo baya kenan

Abuja – Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023, ya yi kira ga manoma su guji ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.

Kamar yadda rahoto ya zo daga Premium Times Darektan sashen noma na kwamitin takaran Bola Tinubu ya yi zama da masu ruwa da tsaki a garin Abuja.

Da yake jawabi a hedikwatar kamfe a ranar Alhamis, Abubakar U. Bello ya ce bai dace manoma su kawo wanda zai dawo da hannun agogo baya ba.

Kara karanta wannan

Wike Ya Umurci Mabiyansa Su Yiwa Bola Tinubu na APC Aiki, Kwamitin Kamfen PDP

An ji Abubakar Bello yana gargadin jama’a cewa akwai ‘dan takaran da yake alkawarin zai bude iyakokin kasar nan, ya ce yin hakan hadari ne.

Hadarin bude iyakoki - PCC

Darektan kwamitin neman zaben yake cewa wannan zai jawo a koma ana shigo da shinkafa, sannan a rika kawo makamai, matasa su rasa ayyukan yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce kwamitin ya ankarar da manoman a kan manufofin wannan ‘dan takara, ya ce ganin illar haka, zai fi kyau a marawa Bola Tinubu baya.

Bola Tinubu
Bola Tinubu yana kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Sakataren kwamitin, Retson Tedheke ya ce Bola Tinubu ba zai yi wasa da noma ba, baya ga neman kudi, zai dauke shi a matsayin harkar inganta tsaro.

The Nation ta ce Ministan harkar gona da raya karkara, Mohammad Abubakar, ya yi jawabi a wajen zaman da aka yi da manoma domin samun kuri’unsu.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Mohammad Abubakar ya yi bayanin nasarorin da aka samu a harkar a karkashin gwamnatin APC, ana ikirarin manoma sun yi kudi sosai a mulkin nan.

Matsayar Atiku Abubakar a kan iyakoki

A baya an samu labarin Atiku Abubakar yana kamfe da cewa zai bude iyakokin kasar idan ya zama shugaban kasa domin rage talauci da bunkasa kasuwanci.

A matsayinsa na tsohon jami’in kwastam, ‘dan takaran na PDP yana tunkahon ya fi sauran abokan gwabzawarsa a 2023 sanin yadda iyakokin kasa suke aiki.

Wanda ya dace a zaba - Sultan, CAN

Rahoto ya fito cewa an shirya taro na musamman domin ganin an samu zaman lafiya tsakanin addinai da ke Najeriya, ganin cewa zaben 2023 ya gabato.

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya yi amfani da damar nan wajen kira ga mabiya da su guji nuna kabilanci a wajen zaben ‘yan takaransu.

Kara karanta wannan

Tinubu Gida-gida: Yadda Aka Gudanar Gangamin Tallata Tinubu Da Shettima Har Gida Ga Mazauna Wata Jahar Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng