Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Yi Maganar Yiwuwar Hadewar NNPP da Atiku

Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Yi Maganar Yiwuwar Hadewar NNPP da Atiku

  • Injiniya Buba Galadima ya maida martani a kan wasu kalamai da ake cewa Atiku Abubakar ya yi
  • Jigon na jam’iyyar PDP ya ce babu yiwuwar Rabiu Kwankwaso ya marawa Atiku baya a zaben 2023
  • Idan har wani zai hakura ya janye takararsa, Buba Galadima ya ce sai dai Waziri ya bi Kwankwaso

Kano - Injiniya Buba Galadima wanda yana cikin jagororin jam’iyyar hamayya ta NNPP ya musanya batun hada-kai da PDP a zaben shugaban kasa.

A wata zantawa da aka fitar a gidan rediyon Rahama da ke garin Kano, Buba Galadima ya ce babu yiwuwar Rabiu Musa Kwankwaso ya taimaki PDP.

Injiniya Galadima yake cewa wani tsohon Ministan shari’a ya fara turo masa sautin da ake zargin na Atiku Abubakar ne, inda aka ji ya yi batun hadin-kai.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Kwararren ‘dan siyasar yake cewa yana zargin ba Atiku ba ne ya fadi maganar domin kuwa ya sani sarai bai taba zama da Dr. Kwankwaso a kan batun ba.

A ganinsa, ‘dan takaran na PDP ya zautu idan yana tunanin jagoran Kwankwasiyya zai bi shi.

Babu maganar janye takara a yanzu

A hirar da aka yi da shi a ranar Alhamis, Legit.ng Hausa ta ji tsohon jigon na jam’iyyar APC yana mai cewa ‘Dan takaransu ba zai janyewa kowa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Oyo Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Galadima ya ce idan har wani zai janye, sai dai Atiku Abubakar ya goyi bayan takarar Kwankwaso domin kuwa a cewarsa, shi ne wanda al’umma suke kauna.

“Ka duba irin hanyoyi da daji da sako-sako da muke bi a kasa. Mun bar Abuja ranar Juma’a da karfe 6:00 na safe, kafin mu je New Bussa inda za mu sauka mu kwana, sai bayan karfe 2:00 na dare.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban Kasa: Ka Janyewa Rabiu Kwankwaso: NNPP Ta yi Kira ga Atiku

Mun tashi daga masaukinmu karfe 10:00 na safe da niyyar za mu wani gari wai Okuta, mu bi ta Kaiama, mu tafi. Ba mu isa garin ba sai washegari da karfe 8:30, ko sallah a daji ba mu samu mun yi ba.
Kuma duka inda mu ka je, ka na ganin irin al’ummar da suke tare su na jiranmu, ba su gaji ba balle mu mu gaji da mu ke tafiya a mota, mu nuna mun gaji. Wannan sarki mun same shi tun jiya har zuwanmu.

- Injiniya Buba Galadima

Atiku zai marawa NNPP baya?

A labarin da ‘dan majalisar BOT na NNPP ya bada, sai da suka yi kwana biyu a hanya a tafiyar karshe da suka yi zuwa wasu garuruwan Arewa ta tsakiya.

Injiniyan ya ce babu ta yadda Kwankwaso da mutanensa za su yu irin wannan fadi-tashi, sannan su goyi bayan Atiku Abubakar da PDP su dare mulki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya

Ana yakin cikin gida a APC

Ku na da labari zargin cin dunduniyar ‘Dan takaran APC a zaben 2023 yana fitowa baro-baro, amma Muhammadu Buhari ya dage a kan ayi zaben gaskiya.

Jiga-jigan APC irinsu Gwamna Nasir El-Rufai sun ce ana yakar Bola Tinubu a cikin gida, a ganinsu saboda haka ake fito da wasu tsare-tsaren tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng