Muhimman Abubuwa 6 da ya Dace a Sani Game da Abba Gida-gida, 'Dan Takarar Gwamnan Kano a NNPP

Muhimman Abubuwa 6 da ya Dace a Sani Game da Abba Gida-gida, 'Dan Takarar Gwamnan Kano a NNPP

Kano - Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, shi ne 'dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar NNPP.

Abba Kabir Yusuf
Muhimman Abubuwa 6 da ya Dace a Sani Game da Abba Gida-gida, 'Dan Takarar Gwamnan Kano a NNPP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yana daya daga cikin 'yan takarar gwamnan jihar da suka halarci muhawarar Media Trust ta 'yan takarar Gwamna da za a yi a dakin taro na BUK a ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairun 2023.

Ga abubuwan da ya dace ku sani game da Abba Kabir Yusuf.

Haihuwarsa da karatunsa

An haife shi cikin iyalan Malam Kabiru Yusuf da Malama Khadijatul-Naja'atu a karamar hukumar gaya ta jihar Kano a ranar 5 ga watan Janairun 1963, Abba ya halatci makarantar Firamare ta Sumaila tsakanin 1968 zuwa 1975.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya cigaba zuwa makarantar sakandaren Gwamnati ta Dawakin Tofa inda daga bisani ya koma makarantar sakandaren Gwamnati ta Lautai da ke Gumel inda ya kammala karatunsa na sakandare a 1980.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Abba Kabir Yusuf ya kammala dufuloma ta farko a Foliteknik dind Mubi a 1985 da babbar dufuloma ta biyu a Civil Engineering aga foliteknik din Kaduna 1989.

Daga bisani ya samu digirin digir a fannin kasuwanci a jami'ar Bayero da ke Kano.

Jinin sarauta

Kakan Abba Gaida-Gida, Alhaji Yusuf Bashari, wanda 'dan takarar gwamnan ya fara karatun addini a wurinsa, shi ne Danmakwayon Kano kuma tsohon hakimin Gaya.

Aiki

Abba Gida-Gida ya fara aiki da hukumar ruwa ta jihar Kano, WRECA inda daga bisani ya koma ma'aikatar ruwa inda ya rike mukamai masu yawa.

Mukaman siyasa

An zabe shi matsayin mataimaki na musamman ga tsohon Gwamnan jihar Kani, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsakanin 1999 zuwa 2003.

Abba yayi aiki da Kwankwaso daga 2003 zuwa 2006 yayin da tsohon gwamnan Kanon ya ke ministan tsaro.

Yayi aiki matsayin mataimaki na musamman ga mai bada shawara ga shugaban kasa Najeriya a Darfur/Somalia har zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Kada ku sake kara wa'adin daina amfani da Naira, Atiku ga CBN

Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar'adu ya nada Abba shugaban kwamitin gudanarwa na NIEPA a jihar Ondo daga 2009 zuwa 2011.

Yayin mulkin Kwankwaso karo na biyu, na nada Abba matsayin PPS na gwamna kuma ya koma kwamishina ayyuka, gidaje kuma sufuri.

Fitowarsa

Takarar da yayi a zaben Gwamnoni na 2019 a Kano wanda aka yi karo batta tsakanin PDP da APC ya fito da Abba Gida-Gida.

'Dan takarar Kwankwason ya buga da Gwamna da ke kan gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a zaben da aka bayyana inconclusive sannan aka lallasa shi bayan an sake zabe.

FG tayi martani ga El-Rufai kan masu makarkashiya ga Tinubu a Aso Villa

A wani labari na daban, Ministan yada labari Lai Mohammed, ya musanta ikirarin Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna na cewa wasu a fadar Buhari na makarkashiya ga Bola Ahmed Tinubu.

Yace Buhari ya mayar da hankali ne wurin tabbatar da an yi zabe na gaskiya a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel