'Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Kamfen din Gwamnan Oyo, Sun Lalata Ababen Hawa

'Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Kamfen din Gwamnan Oyo, Sun Lalata Ababen Hawa

  • Wasu rikakkun 'yan daba sun tare tawagar Gwamna Makinde bayan sun dawo kamfen, sun bukaci ya basu kudi a kan titi
  • Ganin ba zasu samu ba yasa suka dinga jifan motocinsu da sanduna da duwatsu inda daga bisani suka fito da bindigogi suka dinga harbi
  • Hadimin Makinde a fannin yada labarai ya sanar da cewa, sun lalata ababen hawa masu tarin yawa daga cikin na tawagar

Oyo - Wasu da ake kayuata zaton 'yan daba ne sun farmaki tawagar kamfen din 'dan takarar kujerar gwamnan Oyo kuma Gwamnan jihar mia ci yanzu, Seyi Makinde, jaridar The Cable ta rahoto.

Gwamna Makinde
'Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Kamfen din Gwamnan Oyo, Sun Lalata Ababen Hawa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Moses Alao, hadimi na musamman ga gwamnan kan yada labarai, a wata takarda da ya fitar ranar Laraba, yace farmakin ya faru ne a ranar Talata a Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta arewa a jihar.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: An gano sunayen makiyaya 37 da jirgin sojin sama ya babbaka a jihar Arewa

Alao yace gwamnan yayi jawabi ga gagrumin taron jama'a a dakin taron Igangan kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Tapa yayin da lamarin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa, tawagar gwamnan ta ci karo da duwatsu kan titi inda 'yan ta'addan suka bukaci a basu kudi.

Yace 'yan daban sun fara jifan tawagar da sanduna da duwatsu wanda daga bisani suka harbi motocin.

"'Yan adawa ne suka shirya tare da hada wannan farmaki, su ne suka yi hayar 'ya'yan titi domin su hari tawagar gwamnan."

- Alao yace

“Wannan duk an yi ne don batawa gwamnan suna a cikin tsarin jama'ar da ke jihar Oyo. Sai dai ba a yi nasara ba tunda jama'ar jihar sun san Makinde mutum ne mai son zaman lafiya."

- Ya kara da cewa.

Alao yace motar bas JAC da ke dauke da hadiman gwamnan na yada labarai, 'yan jarida da sauran ababen hawan duk 'yan daban sun lalata su.

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

"Zuwa wani lokaci, 'yan daban sun daina jifa da sanduna da duwatsu, sun fito da bindigu tare da harbin tawagarmu.
"Muna da tabbacin wadannan 'yan daban ne suka shiga garin Igangan tare da aiwatar da barna.
“Yayin da muke jajantawa iyalai da wadanda lamarin ya shafa, yana da matukar muhimmanci a gane cewa Gwamna Makinde mutum ne mai son zaman lafiya. Ya bayyana cewa burinsa bai kai matsayin zubar jin jama'ar Oyo ba."

- Yace.

'Yan bindiga sun tashi caji ofis da ofishin INEc da bam a Anambra

A wani labari na daban, wasu miyagun 'yan bindiga sun tada bam a caji ofis da ofishin hukumar zabe a jihar Anambra.

Basu tsaya nan ba, sun budewa jama'a mazauna yankin wuta inda suka harbe mutum daya har lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel