2023: Abinda Atiku Zai Yi Wa Nnamdi Kanu Idan Ya Zama Shugaban Kasa, Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Magantu

2023: Abinda Atiku Zai Yi Wa Nnamdi Kanu Idan Ya Zama Shugaban Kasa, Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Magantu

  • An bayyana daya daga cikin manyan matakan da Atiku Abubakar zai dauka kan jagoran kungiyar masu fafutukar kafa Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu
  • Babban daraktan kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa a Jihar Anambra, Prof. Obiora Okonkwo ya bayyana cewa Atiku zai saki Nmandi Kanu idan ya karbi ragama a matsayin shugaban Najeriya
  • Gabanin babban zaben 2023, Okonkwo ya kara bayyana cewa dan takarar na PDP zai dogara da hukuncin kotun daukaka kara da ta bada umarnin a saki Kanu

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a wata mai kamawa, Atiku Abubakar, zai bada umarnin a sake jagoran kungiyar masu fafutukar kafa Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ba tare da ya sanya sharadi ba, idan ya zama shugaban kasa a 29 ga watan Mayu, a cewar daya daga cikin manyan daraktocin yakin neman zabensa.

Kara karanta wannan

Subut da baka: Atiku ya tabo Tinubu, ya caccaki yadda ya tafka katobara a idon jama'a

Babban daraktan kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa a Jihar Anambra, Prof. Obiora Okonkwo, da ya bayyana lamarin, ya ce Atiku zai yi dogaro da umarnin da kotun daukaka kara tayi na sakin jagoran Biafra.

Atiku, Okowa
2023: Abin Da Atiku Zai Yi Wa Nnamdi Kanu Idan Ya Zama Shugaban Kasa, Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ya Magantu. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Okonkwo, ya bayyana cewa kotun daukaka kara ta yi kakkausan gargadi cewa lallai a saki Kanu kuma kada wata kotu ta sake tuhumarsa da makamancin laifin da yake tsare saboda shi, kamar yadda rahoton Leadership ya tabbatar.

Jigon na PDP ya kuma bayyana cewa daga cikin manyan ayyukan da Atiku ya sa a gaba akwai 'tabbatar da zaman lafiya' a sassan kasar nan musamman Kudu maso Gabas, rahoton Daily Trust ya yi karin bayani.

Sanatan PDP ya bayyana wata tattaunawar sirri da Nmandi Kanu, da abin da zai faru a Kudu maso gabas

Kara karanta wannan

Ahaf: An kuma, Tunubu ya sake yin wata katobarar da tafi na baya game da Atiku

Tashe-tashen hankulan da yake faruwa kudu maso gabas wasu tsiraru ke daukar nauyi kuma hakan bazai shafi gudanar da zabe a yankin ba, a cewar Sanata Enyinnaya Abaribe.

Da yake tattaunawa a gidan talabijin na Channels ranar Laraba, 25 ga Janairu, Abaribe, da ya ke wakiltar Abia ta Kudu, ya bayyana cewa duk da wani lokacin rikicin cikin gida ne, wasu ne suke daukar nauyi daga bayan fage.

Dan siyasar ya bayyana cewa mutanen yankin ba masu son rikici bane, tare da bayyana cewa a hirarsa da Nmandi Kanu, jagoran na IPOB ya bayyana masa babu wani abu wai zaman gidan dole.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164