Yadda Jagororin PDP Suka Yi Banza da Atiku Yayin da Ya Zo Kamfe a Arewacin Najeriya
- Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa sun ziyarci jihar Kebbi domin yakin neman zaben shugaban kasa
- Rikicin cikin gidan da yake damun jam’iyyar PDP ya yi tasiri a wajen taron da aka shirya a birnin Kebbi
- Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayyar a Kebbi ba su je tarbar Atiku ko su halarci yawon kamfe da ya zo ba
Kebbi - Manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP na reshen jihar Kebbi sun kauracewa taron Atiku Abubakar na yakin zaben shugabancin kasa.
Rahoton The Nation ya bayyana cewa da-dama daga cikin shugabannin PDP ba su je taron da aka yi a garin Birnin Kebbi a karshen makon da ya wuce ba.
Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya da abokin takararsa watau Ifeanyi Okowa sun ci karo da rikicin cikin gidan da ake yi a jihar Kebbi.
Abin da ya jawo sabanin shi ne ana zargin jam’iyyar adawar da fifita wasu daga cikin tsofaffin ‘ya ‘yan APC da suka sauya-sheka a kan asalin ‘ya 'yan PDP.
Wadanda suka sha kashi a yakin neman zaben APC sun samu tikitin takara daga dawowarsu PDP. Rahoton ya ce wannan ya jawo ake ta shari’a a kotu.
Su wa suka halarci taron?
Manyan ‘yan PDP da suka je taron kamfen da aka yi sun hada da tsofaffin Ministoci irinsu, Samaila Sa’idu Samabawa, Kabiru Tanimu da kuma Buhari Bala.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Laftana Janar Ishaya Bamayi (retd.), Manjo Janar Bello Sarkin Yaki (retd.), da ‘yan takara; Ibrahim Manga, Sani Bawa, Haruna Saidu sun halarci gangamin.
Baya ga wadannan, akwai jiga-jigan PDP da-dama ba su taka kafarsu zuwa wajen yakin neman zaben da aka shirya a filin sukuwa da ke birnin Kebbi ba.
Zan bude iyakoki - Atiku
Independent ta rahoto cewa Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin bude duka iyakokin kasar nan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta rufe a 2019.
Da yake bayani a wajen taron, Atiku Abubakar ya ce a matsayinsa na tsohon jami’in kwastam, ya fi sauran masu neman takara fahimtar sha’anin iyakoki.
‘Dan takaran PDP ya na zargin rufe iyakokin da aka yi ya takaita kasuwanci da jawo rashin aiki.
Buhari bai adalci - Olusegun Obasanjo
Rahoto ya zo da aka ji Olusegun Obasanjo yana tuhumar Gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta da son kai da rashin adalci wajen nada mukamai.
Olusegun Obasanjo ya ce a tarihi ba a taba yin lokacin da siyasa ta raba al’umma ta fuskar addini da kabilanci irin yanzu ba, saboda son kan shugabanni.
Asali: Legit.ng