Obasanjo: Yadda Shugaba Buhari Ya Raba Kan Al’umma Da Gan-Gan a Gwamnatinsa

Obasanjo: Yadda Shugaba Buhari Ya Raba Kan Al’umma Da Gan-Gan a Gwamnatinsa

  • Olusegun Obasanjo yana ganin babu adalci wajen yadda Muhammadu Buhari yake nada mukamai
  • Tsohon Shugaban Najeriya ya ce ana duba abokantaka a maimakon sanin aiki wajen rabon kujeru
  • Obasanjo ya ce jawo tarkace a Gwamnati a maimakon a rika damawa da kowa ya jawo hadari sosai

Kaduna - Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya zargi shugabanni da jefa kasa a cikin hadari da barazana a dalilin son kan da suke yi.

Punch ta rahoto Olusegun Obasanjo yana mai kokawa da cewa ana rabon mukaman gwamnati ba tare da an yi adalci ba, ya na zargin ana nuna son kai.

Obasanjo ya tuhumi Gwamnatin Muhammadu Buhari da zaben na kusa da ita ta na daura su a kujerun gwamnati, a maimakon ayi la’akari da cancanta.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan bayani da ya ke gabatar da jawabinsa kan muhimmancin makarantun gwamnati wajen kawo hadin-kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Obasanjo ya ziyarci Kaduna

Rahoton ya ce Obasanjo ya gabatar da jawabi ne a makarantar sakataren gwamnatin tarayya da ke Kaduna a wajen bikin makarantar shekaru 50 da kafuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A maimakon a rika tafiya da kowa a wajen yin rabon kujeru da mukamai, Obasanjo ya ce gwamnatoci, ‘yan siyasa da jam’iyyu wasu abubuwan suke kallo.

Obasanjo
Shugaba Obasanjo a Amurka Hoto: www.usip.org
Asali: UGC

Da yake bayani a garin Kaduna, The Cable ta ce tsohon shugaban na Najeriya ya koka a game da tattalin arziki, ya ce talauci ya karu, farashin kaya sun tashi.

"Baya ga matsin lambar tattalin arziki akwai barnar ‘yan siyasa. Ba a taba yin lokacin da siyasa ta raba al’umma ta fuskar addini da kabilanci irin yanzu ba.
Ana raba mukaman gwamnati da son kai ba tare da adalci ba, ana jawo abokai da tarkacen mutane, ayi watsi da sanin aiki da cancantar wadanda za a dauko.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Sannan kuma ga zabe ya karaso, hakan ya kara jagwalgwala lamarin.

- Olusegun Obasanjo

Jaridar ta ce Obasanjo yana zargin cewa da gan-gan aka yi haka, ‘yan siyasa da jam’iyyunsu sun watsar da tsarin da ake bi na adalci, sun kawo son ra’ayinsu.

Dalili zuwa na Soja - Buhari

An samu labari cewa yayin da ya je jihar Katsina, Mai girma Muhammadu Buhari ya ziyarci fadar Mai marraba Sarkin Daura a ranar Juma'ar da ta wuce.

Shugaban kasar ya bada tarihin shigansa soja da ya fahimci ana son yi masa aure da wuri. A shekarar 1961 Buhari ya zama Soja, ya yi watsi da aikin shago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng