Ba Zan Bar Gidana Na Koma Dauji, Shugaban Majalisa Ya Karyata Komawa PDP
- Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya yace yana nan daram a jam'iyyar APC babu inda zai koma
- Sanata Ibarim Gobir daga mazaɓar gabashin Sakkwato ya ce raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa zai koma PDP kafin zaɓe karya ne
- Yace ba ta yadda za'ai ya bar gidansa ɗaya tilo ya koma kwana a Jeji, yana nan tare da 'yan takarar APC
Sokoto- Sanata Ibrahim Gobir mai wakiltar Sakkwato ta gabas ya bayyana cewa yana nan daram a jam'iyyar APC sabanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai koma PDP gabanin babban zaɓen 2023.
Vanguard ta tattaro cewa Gobir, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa kuma shugaban Sanatocin APC, ya musanta raɗe-raɗin ne yayin hira da 'yan jarida a Sokoto ranar Lahadi.
Legit.ng Hausa ta gano cewa Sanatan ya nemi tikitin takarar gwamnan APC a zaben fidda gwani da ya gudana a Sakkawato. Yace APC ce gida ɗaya tilo da ya mallaka kuma ba abinda zai fitar da shi.
Sanatan yace:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Jita-jitar da ake yaɗawa cewa Sanata Gobir na shirin barin APC ƙaryane, na bar gidana na koma Jeji ko kuwa ya kenan? Bana tsalle-tsalle daga jam'iyya zuwa wata."
"Bugu da kari ko na samu damar takara ko ban samu ba, ba zai yuwu na tashi daga wurin da nake ba haka nan kawai ina zaune lafiya a gidana."
"Saboda haka ni ɗan APC ne kuma zan ci gaba da goyon bayan 'yan takararmu domin tabbatar da jam'iyyarmu ta samu nasara a babban zaben 2023 don kyaun goben talakawa da demokaradiyya."
Gobir ya kara da cewa yanayin siyasar Najeriya ya nuna cewa APC ce jam'iyyar da zata ci gaba da jan ragamar ƙasar nan duba da yadda mutane suka yi na'am da ita.
"Bisa la'akari da yadda mutane ke tururuwar sauya sheƙa zuwa jam'iyyarmu zan bugi ƙirji na ce gaba ɗaya yan takararmu jiran rantsarwa suke ranar 29 ga watan Mayu, 2023."
'Yan Kwankwasiyya Sun Kona Jar Hula, Sun Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023
A wani labarin kuma 'Yan Kwankwasiyya Sun Kona Jar Hula, Sun Suaya sheƙa zuwa zuwa jam'iyyar APC nai mulki
Mutanen suna cikin mambobin siyasa 10,000 daga PDP, NNPP, ADC da wasu jam'iyyu waɗanda suka sauya sheka zuwa APC
Mutanen sun kuma ayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu .
Asali: Legit.ng