Mun karbi tsoffin kudi Tiriliyan N1.9tr, Saura N500bn a hannun Mutane, CBN

Mun karbi tsoffin kudi Tiriliyan N1.9tr, Saura N500bn a hannun Mutane, CBN

  • Babban bankin Najeriya ya bayyana makudan kudaden da yan Najeriya suka maida bankuna zuwa yanzu
  • A ɗazu ne aka ji gwamnan CBN na faɗin shugaban ƙasa ya amince da kara wa'adin amfani da tsoffin kuɗi
  • Godwin Emefiele yace sun karbi kusan Tiriliyan biyu daga hannun jama'a abinda suke tsammanin saura basu kai haka ba

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa jumullan tsoffin kuɗi Tiriliyan N1.9trn sun dawo hannun bankuna, abinda ya rage bai wuce N900bn ba a hannun Jama'a.

The Cable ta rahoto cewa cewa gwamnan bai ce komai ba game da tsarin da suke yi na adadin yawan sabbin kuɗin da zasu sakarwa jama'a a yanzu.

Gwamnan CBN.
Mun karbi tsoffin kudo Tiriliyan N1.9tr, Saura N500bn a hannun Mutane, CBN Hoto: thecable
Asali: Getty Images

A ranar Lahadin nan Bankin ya ƙara wa'adin sauya tsoffin takardun kuɗi da karɓan sabbi daga 31 ga watan Janairu, 2023 zuwa 10 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

CBN Ya Tsawaita Lokacin Amfani da Tsohon Kudi, An Bada Sabon Wa’adi a Najeriya

Haka zalika duk wanda bai samu damar maida tsaffin kuɗin ba har sabon wa'adin ya cika to yana da karin mako ɗaya ya hanzarta kai su kai tsaye ga CBN.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Emefiele ya ƙara da cewa bayan ranar 17 ga watan Fabrairu, duk wata takardar tsohon kuɗi N200, N500 da N1000 zata zama takarda mara amfani, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A jawabin da ya yi ga manema labarai ranar Lahadi, Gwamnan CBN ya ce:

"A bayanan da CBN ke da su, a 2015 kuɗin da mutane ke hada-hada dasu basu wuce N1.4 Tiriliyan ba, amma zuwa watan Oktoba, 2022 kuɗin sun ɗaga zuwa N3.23 Tiriliyan."
"Daga cikin waɗan nan kudi, biliyan N500bn ne kaɗai ake hada-hada da su a bankuna yayin da sauran Tiriliyan N2.7trn suke a gidajen mutane jibge."

Kara karanta wannan

Saura Kwana 2 Wa'adi Ya Cika, CBN Ya Ɓullo da Shirin Yadda 'Yan Arewa Zasu Samu Sabbin Kuɗi Cikin Sauki

"Tun daga fara wannan sabon tsarin, mun karbi kusan Tiriliyan N1.9trn, abinda ya rage mana bai wuce Biliyan N900bn ba."

Game da raba sabbin takardun kuɗin da CBN ta canja, Gwamnan ya ce babban bankin ƙasa ya ɗauki matakai da dama domin kar yan Najeriya su shiga mawuyacin hali.

CBN ya fara shirin musayar kuɗi

A wani labarin kuma Babban Bankin ƙasa ya tantance wakilai 400 da zasu shiga kurfa-kurfa su raba wa mutane sabbin kuɗi

Daraktan sashin dabaru na CBN ga bayyana cewa wakilan zasu shiga lungu da sako su karɓi tsoffin kuɗi hannun jama'a su musanya masu da sabbi a jihar Kogi.

Ya ce daga yanzu kowane mutum na da ikon zuwa Bankuna ko wurin waɗan nan wakilan domin ya musanya tsoffin kudinsa da sababbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel