2023: Dan Majalisar Wakilan Tarayya Daga Katsina Ya Fice Daga Jam'iyar A APC
- Ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Katsina, Hamza Dalhat, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki
- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ya aikewa shugaban APC na gundumar Batagarawa A watau mahaifarsa
- Duk da bai bayyana dalilin ɗaukar matakin nan ba ana tsammanin a gobe Litinin PDP zata masa maraba zuwa cikinta
Katsina - Mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Batagarawa, Rimi da Charanchi, jihar Katsina, Honorabul Hamza Dalhat, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.
Jaridar Vanguard ta rauwaito cewa ɗan majalisar ya bayyana matakin da ya ɗauka a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban APC na gundumar Batagarawa A inda ya fito.
Hamza, wanda ya rasa tikitin tazarce kan kujerarsa a APC, bai faɗi maƙasuɗin da ya sa ya fita daga jam'iyya mai mulki a ƙurarren lokaci da zaɓe ya ƙara matsowa.
Wasu bayanai da aka tattara sun nuna cewa a ranar Litinin mai zuwa jam'iyyar PDP reshen Katsina zata tarbi ɗan majlisar tarayyan a hukumance.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wasiƙar wacce ya yi wa take da, "Sanar da matakin fita daga APC" ta ce:
"Na rubuta wannan wasika ne domin na sanar maka matakin da na ɗauka na ficewa daga jam'iyyar All Progressives Congress daga ranar da na rubuta wannan takarda."
"Katin mamban APC na haɗe da wannan wasika. Ina amfani da wannan dama wajen miƙa godiya da jinjina ga jam'iyya da mambobinta waɗanda suka taimaka a ɓoye ko fili wajen ganin ban manta da zama na da su ba."
"Ina kuma ƙara amfani da wannan dama na miƙa godiya da magoya baya da ɗaukacin mutanen mazaɓar Batagarawa, Rimi da Charanchi saboda amince mun na ba da gudummuwata wajen gina ƙasa a wa'adin zamana a majalisa."
Atiku ya kara kafuwa a shiyyoyin kudu guda biyu
A wani labarin kuma Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Marawa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu
Jam'iyyun sun sha alwashin yin aiki tukuru domin nasarar ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da abokin gaminsa, gwamna Okowa.
Wannan na zuwa ne kwanaki ƙasa da 30 gabanin babban zaben shugaban ƙasa wanda INEC ta tsara gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Asali: Legit.ng