Rayuka Sun Salwanta Yayin da Mambobin PDP da APC Suka Kacame da Faɗa a Osun

Rayuka Sun Salwanta Yayin da Mambobin PDP da APC Suka Kacame da Faɗa a Osun

  • Magoya bayan APC da PDP sun kacame da faɗa a Ikire ta jihar Osun yayin da suka je kamfen ɗan takarar Sanata
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da Ralin yan takarar Sanatan APC da PDP ya haɗu rana ɗaya
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan Osun ya tabbatar da cewa an samu rasa rai wasu na Asibiti

Osun - Mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata biyo bayan wata rigima da ta haɗa magoya bayan PDP da APC a garin Ikire, jihar Osun.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a gaban Ɗan takarar Sanatan Osun ta yamma na APC, Amidu Tadese, da abokin hamayyarsa na PDP, Lere Oyewumi.

Rikicin siyasa.
Rayuka Sun Salwanta Yayin da Mambobin PDP da APC Suka Kacame da Faɗa a Osun Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa 'yan takaran biyu sun zabi lokacin gangamin kamfensu na Ikere a rana ɗaya. Tadese ya ce Oyewumi ne ya ja tawagar yan daba suka kai masa farmaki har wurin taro.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Harbawa Mutane Bama-Baman Roka a Jihar Zamfara

Mista Tadese ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Magoya bayanmu sun shirya runfuna sun tsaya a gunduma ta 9, Ikire kafin faruwar lamarin. Muna gab da farawa muka hangi yan daba suna harbi kan mai uwa da wabi."
"Sun haura su 30 bisa jagorancin dan takarar Sanatan PDP a Osun ta yamma, Akogun Lere Oyewumi. Suna ta harbi ba kakkautawa kafin mu ankara sun iso inda muke."
"Nan suka fara bugun mutane suna lalata mana kayayyaki har da Motocin mu da Bas da Keke Napep."

Mambobin APC suka fara kai mana hari

Amma a nasa jawabin, Mista Oyewumi, yace mambobin APC ne suka kai masa farmaki suka kashe magoya bayansa guda biyu.

Jaridar Punch ta rahoto Oyewumi na cewa:

"Yan daban APC ne suka kawo mana hari muna hanyar zuwa Rali da daddare kuma sun kashe mana mutane 2 yayin da wasu ke kwance a Asibiti suna karban magani."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Saura kiris zabe, dan takarar gwamnan PDP a wata jiha ya kwanta dana

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace an kashe wasu yayin wasu ke kwance a Asibiti.

A wani labarin kuma Gwamnan Bayelsa ya bayyana kokarin da suke yi na ganin Kwankwaso ya dawo gidan da aka sanshi watau PDP

Gwamna Diri ya ce shi da wasu manyan yan siyasa a Najeriya na ci gaba da Addu'a domin tsohon gwamnan Kano ya dawo a haɗa kai.

A cewar gwamnan Kwankwaso cikakken ɗan siyasa ne amma a zahiri PDP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel