Hantar Magoya Bayan Atiku Za ta Kada, Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Kus-Kus da Shettima

Hantar Magoya Bayan Atiku Za ta Kada, Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Kus-Kus da Shettima

  • Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya karbi bakuncin Kashim Shettima da mutanensa
  • ‘Dan takaran na mataimakin shugaban kasa a APC ya ziyarci jigon ‘yan adawar a gidansa da ke Abuja
  • Ana tunanin Sanata Shettima ya fara yi wa jam’iyya mai mulki zawarcin tsohon Gwamnan na PDP ne

Abuja - ‘Dan takaran kujerar mataimakin shugaban Najeriya a APC, Kashim Shettima ya kai ziyara ta musamman zuwa wajen Mista Ayodele Fayose.

Kamar yadda Kashim Shettima ya sanar a shafukansa na sada zumunta, shi da kan shi ya je har gidan tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

A yammacin Talata ne Sanata Shettima ya je gidan Fayose, kuma an ga sun dauki hotuna cikin fara’a, amma ba a san makasudin tattaunawar ba.

“Na kai wa ‘danuwa, tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Mai girma Ayodele Peter Fayose ziyara. Oshoko ya karbe hannu biyu-biyu cikin abokantaka.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

“Na gode da goyon bayanka, Ubangiji ya yi maka sakayya da ka karbi bakunci na tare da ‘yan tawaga ta.

- Kashim Shettima

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ayo Fayose
Ayo Fayose da Kashim Shettima Hoto: kashimshettima.org
Asali: Facebook

Me ya kai Kashim Shettima wajen Fayose?

Jaridar Premium Times ta ce wannan lamari ya jawo mutane su na tofa albarkacin bakinsu a kan shafin Facebook na tsohon Gwamnan na jihar Borno.

Kiran Fayose wanda ya yi suna wajen adawa ga gwamnatin APC da Muhammadu Buhari yake jagoranta da ‘danuwa ya sa ake tunanin ana zawarcinsa.

Fayose yana cikin gwamnonin da ke yakar Iyorchia Ayu a kan takarar Atiku/Okowa.

Rikicin cikin gidan PDP a Ekiti

Kwanan nan shugabannin PDP suka dakatar da wasu mabiyansa da ke takara, sannan aka ruguza majalisar shugabannin jam’iyya na reshen Ekiti.

Babu mamaki Shettima ya yi amfani da rikicin cikin gidan na PDP ne domin ya jawo Fayose zuwa jam’iyyar APC da nufin ya taimaka masu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna Kuma Farfesa Ya Bayyana Mutum Ɗaya Tilo da Zai Iya Ceto Najeriya a 2023

Punch ta fitar da labarin ganawar, kuma har zuwa yanzu ba a ji komai daga bakin Fayose ba.

A tsige Festus Keyamo - PDP

Rahoto ya zo cewa Jam’iyyar PDP ta dage cewa sai an sauke Festus Keyamo SAN. A lokacin ne Shugaban kasa yake taya Ministan murnar cika shekaru 53.

Kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar ya tuhumi Keyamo da cin amanar da aka damka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng