Ku Tuhume Ni Idan Miji Na Bai Tsinana Muku Komai Ba, Cewar Titi Atiku, Matar Dan Takarar PDP

Ku Tuhume Ni Idan Miji Na Bai Tsinana Muku Komai Ba, Cewar Titi Atiku, Matar Dan Takarar PDP

  • Uwargidan dan takarar shugaban kasa a PDP ta bayyana abin da za a yi mata idan mijinta bai tsinana komai ba
  • Titi Atiku Abubakar ta bayyana abubuwan da ta shirya yiwa mata da kananan yara a Najeriya idan suka ci zabe
  • Ta bukaci mata su mallaki katin zabe, kuma su fito a dama dasu a ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa nan kusa

Abeokuta, jihar Ogun - Matar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Mrs Titi Atiku Abubalar ta nemi mata ‘yan Najeria da su tuhume ta matukar mijinta ya gaza cika alkawuran kamfen da ya dauka idan ya gaji Buhari.

Ta bayyana cewa, Atiku ba zai watsar da yankin Kudu maso Yamma ba, domin ba Atiku kuri’u daidai yake da ba Yarbawa kuri’u, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Riba biyu: Daga siyan Zobo mai sanyi, matashi ya yi wuf da mai talla a Twitter, jama'a sun yi mamaki

Ta bayyana wannan ne a wani taron siyasa na mata da aka gudanar a jihar Ogun a birnin Abeokuta na jihar.

Matar Atiku ta ce idan mijinta bai yi aiki ba laifinta ne
Ku Tuhume Ni Idan Miji Na Bai Tsinana Muku Komai Ba, Cewar Titi Atiku, Matar Dan Takarar PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Matar Atiku ta ce, idan aka zabi mijinta, za ta zama Bayarbiya ta farko da ta zama uwar gidan shugaban kasa daga yankin Kudu maso Yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kuma bukaci mata da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’u ga mijinta a zaben 25 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Mijina zai kawo mafita ga matsalolin Najeriya, inji Mrs Titi

Ta kuma bayyana cewa, mijinta zai kawo karshen fatara da rashin tsaro matukar aka zabe shi ya zama shugaban kasa a Najeriya.

Da take magana, shugabar matan PDP ta kasa, Farfesa Stella Effah-Attoe ta bukaci mata da su mallaki katin zabe su rike gam, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Nemo Magani, Ya Bayyana Yadda 'Yan Najeriya Zasu Kawo Karshen Yan Bindiga

Ta bukace su da fito a dama dasu a zaben bana domin ba da kuri’unsu ga Atiku a matsayinsu na ‘yan kasa masu ‘yancin yin zabe.

Ku zabi Atiku, matar dan takarar gwamna ga mata

Uwar gidan dan takarar gwamna a jihar, Adenike Adebutu ta yabawa matar Atiku a tsayawa da take kullum tsayin daka domin tabbatar da an taimaki mata da kananan yara a Najeriya.

Ba wannan ne karon farko da matar Atiku ke cewa mijinta ne ya cancanta ya gaji Buhari ba, ta sha bayyana hakan a baya.

Ta kuma sha yin kira ga Yarbawa da su cika mata burin zama uwar gidan shugaban kasa ta farko daga Kudu maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel