Ba zamu tallata Atiku Abubakar ba a jihar Ribas, Gwamna Wike

Ba zamu tallata Atiku Abubakar ba a jihar Ribas, Gwamna Wike

  • Gwamnan jihar Ribas ya kara jaddada matsayarsa na tsayawa iya ihar Ribas ya yi wa yan takara kamfe
  • Nyesom Wike, ya bayyana cewa zaben gwamna, Sanatoci da yan majalisun tarayya da na jiha duk zai masu kamfe
  • A cewarsa sai mutum ya zo ya nemi ka yi masa kamfe ne zata yi, idan be kawo kansa ba dama babu dole

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada cewa ba zasu tallata Atiku Abubakar ba a yawon yakin neman zaben PDP da suke ci gaba da yi a sassan jihar.

Gwamnan ya ce ba zasu taba yi wa Atiku kamfe ba saboda babu wata yarjejeniya ko fahimtar juna da ta cancanci Ribas ta mara masa baya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamna Wike.
Ba zamu tallata Atiku Abubakar ba a jihar Ribas, Gwamna Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Wike ya yi wannan furucin ne a garin Bonny a wurin gangamin yakin neman zaben da kwamitim kamfen PDP na jihar Ribas ya shirya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaka Dauki Kaddara Idan Ka Sha Kaye a 2023? Kwankwaso Ya Ba Da Amsa Mai Jan Hankali

Da yake jawabi ga mutanen Bonny, Wike ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ku koma gida ku sa a ranku cewa mun ɗauki zaɓen gwamna, mun dauki zaben Sanatoci da mambobin majalisar wakilan tarayya, mun ɗauki zaben yan majalisar dokoki."
"Waɗan nan ne zabukan da zamu maida hankali a nan, su ne kaɗai 'yan takarar da suka nemi na fito na taimaka musu da kamfe, babu wani da ya roki na yi masa kamfe."
"Ba zan matsawa kaina dole sai na maka Kamfe ba bayan kai baka zo ka nema ba, waɗan nan ne kaɗai yan takarar da suka nema kuma ga shi na zo nan garin ne na yi kamfe."
"Idan wani ya zo ya roki ka masa aiki zaka yi masa aiki amma idan basu son ka taimaka masu, shin zaka matsa dole sai ka musu aiki?"

Kara karanta wannan

2023: Ka Janye Idan Ka San Ba Ka Da Lafiya, Malamin Addini Ya Gargadi Yan Siyasa, Ya Ce Wani Jigo Zai Mutu

Gwamnan, wanda ke takun saka da Atiku Abubakar na PDP, ya ce duk wanda ke ganin jihar Ribas ba zata iya komai ba to ya shirya wa abinda zai biyo baya idan ya yi watsi da jihar.

Atiku ba zai kai labari ba yankuna 2

A wani labarin kuma Babban Jigon PDP Ya Fadi Jihohin da Atiku Ba Zai Samu Nasara Ba Tare da Dalilai

Tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya ce mai yuwuwa Atiku ba zai kai labari ba a shiyyoyin kudu guda biyu.

A cewar Mista Chidoka, arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya ne zasu yanke wanda zai gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262