Kotu Ta Kori Karar da Jam'iyyar PDP Ta Shigarda Gwamnan Jihar Gombe

Kotu Ta Kori Karar da Jam'iyyar PDP Ta Shigarda Gwamnan Jihar Gombe

  • Babbar Kotun tarayya ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar tana rokon a haramtawa gwamnan Gombe takara a APC
  • PDP da ɗan takararta na gwamna, Mohammed Barde, sun zargi gwamna Inuwa Yahaya na jam'iyar APC da amfani da jabun takardu
  • Da take yanke hukunci, Kotun tace PDP da Barde ba su da hurumin kai Yahaya Kara saboda ba dasu aka gudanar da zaben fidda gwani ba

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a birnin tarayya Abuja ta yi fatali da ƙarar da dan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Mohammed Barde, ya shigar gabanta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ɗan takarar ya shigar da ƙarar gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da wasu biyu yana rokin a kori ɗan takarar APC.

Gwamna Inuwa Yahaya.
Kotu Ta Kori Karar da Jam'iyyar PDP Ta Shigarda Gwamnan Jihar Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

A wata sanarwa da Darakta janar na sashin yaɗa labaran gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Misilli, ya aike wa manema labarai ya ce Kotu ta yi watsi da ƙarar saboda ba shi da hurumin kai INEC ko Yahaya ƙara.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

Idan baku manta ba Barde, mai neman kujerar gwamna na PDP ya maka Yahaya, gwamnan jihar Gombe a gaban Kotu yana tuhumarsa da amfani da jabun takardu, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane hukunci Kotu ta yanke kan Kes ɗin?

A sanarwan da ya fitar yau Talata, 24 ga watan Janairu, 2023, Misilli ya ce:

"Yayin yanke hukunci kan karar da PDP ta shigar da INEC da wasu mutane mai lamba FHC/ABJ/CS/1301/2022, babbar kotun tarayya ta ƙi yarda da hurumin masu ƙara."
"Kuma ta yanke cewa jam'iyyar PDP ko Muhammed Jibrin Barde ba bu ɗayansu dake da hurumin kai ƙarar INEC ko Yahaya saboda ba su fafata a zaben fidda gwanin APC da ya samar da gwamna a matsayin ɗan takara ba. An kori Kes din."

A wani labarin kuma Kotu Ta Umarci a Sauya Zaben Fidda Gwanin APC a Kananan Hukumomi 11 Na Benue

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Ta dauki wannan matakin ne biyo bayan ƙarar da ɗaya daga cikin 'yan takarar APC, Farfesa Terhemba Sjija, ya shigar gabanta yana kalubalantar hukuncin ƙaramar Kotu.

Alkalin Kotun ya bayyana cewa ya amince APC ta gudanar da zaben fidda gwani a kananan hukumomi 12, don haka ta koma ta shirya a sauran yankuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel