Kotu Ta Umarci a Sauya Zaben Fidda Gwanin APC a Kananan Hukumomi 11 Na Benue

Kotu Ta Umarci a Sauya Zaben Fidda Gwanin APC a Kananan Hukumomi 11 Na Benue

  • Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci kan danbarwan tikitin APC na takarar gwamnan jihar Benuwai
  • Alkalin Kotun ya umarci APC ta shirya sabon zaben fidda gwani a kananan hukumomi 11
  • Kotun tace ta yarda APC ta gudanar da zabe a kananan hukumomi 12, don haka ta koma ta gudanar a sauran

Benue - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Makurdi, jihar Benuwai, ta umarci sake shirya zaben fidda ɗan takarar gwamnan APC a kananan hukumomi 11 na jihar.

Jaridar Daily Trust tace Kotun, ranar Litinin, ta kuma ba da umarnin sauya zaben a wuraren da lamarin ya shafa cikin kwanaki 14 masu zuwa.

Jam'iyyar APC.
Kotu Ta Umarci a Sauya Zaben Fidda Gwanin APC a Kananan Hukumomi 11 Na Benue Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ta dauki wannan matakin ne biyo bayan ƙarar da ɗaya daga cikin 'yan takarar APC, Farfesa Terhemba Sjija, ya shigar gabanta yana kalubalantar hukuncin ƙaramar Kotu kan zaben.

Kara karanta wannan

'Babban Abinda Atiku Abubakar Ya Rasa Wanda Ka Iya Jawo Masa Faɗuwa a Zaben 2023'

Hukuncin da Kotun ɗaukaka kara ta yanke

Mai shari'a Gabriel Georgewill ya bayyana cewa ya amince da ikirarin mai ƙara cewa APC ba ta gudanar da zaben fidda ɗan takarar gwamna ba a ranar 27 ga watan Mayu, 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan Alkalin ya kuma amince da jawabin APC cewa ta sake shirya zabe a ranar 9 ga watan Yuni, 2022, wanda ya gudana a kananan hukumomi 12 na jihar Benuwai.

A ruwayar Punch, Mai shari'a Georgewill ya ce:

"Eh na fahimci APC bata shirya zaben ba ranar 27 ga watan Mayu, 2022 shiyasa Kotu ta umarci a sake zabe wanda ya gudana ranar 9 ga watan Yuni, 2022 a wasu kananan hukumomi."
"Saboda adalci, ba zan kyale hakkin mutanen sauran kananan hukumomi 11 ya tafi a banza ba, don haka APC ta koma ta shirya zabe a waɗan nan yankuna cikin kwana 14."

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Baiwa Yan Najeriya Zabi, Ya Tono Wata Yaudara da Buhari Ya Yi a 2019

"Kuma hukumar zaɓe ta karbi sunan wanda ya samu nasara bayan haɗa sakamakon zaben farko da sabon da za'a yi a matsayin ɗan takarar gwamnan APC."

Wane kananan hukumomi ne abun ya shafa?

Legit.ng ta tattaro kananan hukumomin da hukuncin sake zaben ya shafa, wanda ya suka haɗa da, Gboko, Gwer ta gabas, Gwer ta yamma, Guma, Katsina, Logo, Makurdi, Otukpo, Ukum, Tarka da kuma Vandeikya.

A wani labarin kuma Babban Jigon PDP Ya Fadi Jihohin da Atiku Ba Zai Samu Nasara Ba Tare da Dalilai

Tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya ce mai yuwuwa Atiku ba zai kai labari ba a shiyyoyin kudu guda biyu.

A cewar Mista Chidoka, arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya ne zasu yanke wanda zai gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel