Shugabannin SDP a Jihar Legas Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP
- Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP ta samu karin goyon baya a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya
- Shugabannin jam'iyyar SDP reshen jihar Legas sun tattara sun koma PDP, sun ce ɗan takarar gwamna ne ya ja hankalinsu
- Shugaban PDP a jihar ya basu tabbacin cewa ba za'a nuna masu banbanci ba, suna da hakki kamar kowane mamba
Lagos - Shugabar Social Democratic Party (SDP) a jihar Legas, Dabiraoluwa Adeyinka, da wasu mambobin kwamitin zartaswa na jam'iyyar sun sauya sheƙa zuwa PDP.
The Cable tace Adeyinka, wacce ta jagoranci masu sauya shekar zuwa PDP, ta ce gogewar shugabancin da suka hanga jikin ɗan takarar gwamnan PDP na Legas, Abdulazeez Adediran ne ya ja hankalinsu.
A cewarta, ɗan takarar gwamnan da abokiyar takararsa, Funke Akindele su ne kaɗai zabin da ya rage wa mazauna Legas su kori jam'iyyar APC mai mulki, Premium Times ta rahoto.
Da yake maraba da masu sauya shekar a Ofishin kamfe dinsa, Mista Adediran, ya ce 'yan siyasar sun ɗauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ɗan takarar gwamnan, wanda ya fi shahara da Jandor, ya sanar da naɗa Mis Adeyinka a matsayin ɗaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin kamfe ɗinsa.
Bayan haka shugaban PDP na Legas, Philip Aivoji, ya miƙa wa tawagar masu sauya shekar tutar jam'iyya sannan ya tabbatar masu cewa, "Ba zasu ga ko burbushin alamun nuna banbanci ba idan aka kafa gwamnati."
"Ba zaku gamu da halin nuna banbanci ba a cikin inuwar PDP idan muka kai ga kafa gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Muna baku tabbaci da zaran kun shiga PDP kun zama cikakkun mambobi."
"Zaku samu duk wata dama hakkin waɗanda kuka zo kuka taras. Kuna da ikon shiga a dama da ku a dukkan harkokin jam'iyya a matakin gunduma, ƙaramar hukuma da jiha."
Bani da matsala idan na faɗi zaben shugaban kasa, Kwankwaso
A wani labarin kuma Mai neman zama shugaban ƙasa na NNPP ya bayyana matakinsa na gaba idan ya faɗi zaben 2023
Sanata Kwankwaso ya ce a tarihin siyasarsa ya nemi takara sau 18, amma sau uku kaɗai ya yi rashin nasara.
A cewarsa yana matsayin gwamna aka kayar da shi a zabe kuma ya amince, don haka faɗuwa ba sabon abu bane a wurinsa.
Asali: Legit.ng