Yadda Atiku Abubakar Zai Bi Wajen Dankara Tinubu da Peter Obi da Kasa Inji PDP PCC
- Dele Momodu ya fitar da jawabi yana cewa ‘dan takaransu, Atiku Abubakar za a rantsar a Mayun 2023
- Darektan dabarun sadarwa na kwamitin neman zaben Atiku/Okowa ya ce tarihi ya gaskata nasarar PDP
- Momodu ya ce duk lokacin da ‘Dan Arewa da ‘Dan Kudu aka tsaya zabe, mutumin Kudu bai kai labari
Abuja - A kwanakin nan, ana ta jin maganar Dele Momodu wanda shi ne Darektan dabarun sadarwa na kwamitin neman zaben Atiku Abubakar.
Wannan karo, Punch ta rahoto Dele Momodu yana cewa ‘dan takaransu na shugaban kasa watau Atiku Abubakar ne zai yi galaba a zaben da a shirya.
A wani jawabi da Momodu ya fitar a ranar Litinin, ya yi watsi da duk wasu hasashe da aka yi da suka nuna nasarar Peter Obi ko Asiwaju Bola Tinubu.
‘Dan siyasar yake cewa ya karanta hasashe da yawa da aka gudanar a kan zabe, kuma ya gane yadda masu nazarin suke tafka kuskure a aikinsu.
Kuskure da ake yi a hasashe
A cewar Darektan sadarwan kwamitin neman takaran, masu yin wadannan hasashe su na dogara da kafofin fasaha, alhali jahilai sun fi yawa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Momodu ya fitar a jawabinsa, a duk lokacin da Kudu da Arewa suka tsaida ‘yan takaran shugaban kasa, mutumin Arewa yake yin nasara.
1979 yana kama da 2023
Irin haka ya faru tsakanin Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe da Shehu Shagari a 1979 da 1983.
Kwamitin neman takaran yake cewa duk da haka Cif Obafemi Awolowo ya fi Bola Tinubu karbuwa a yankin da ya fito na Kudu maso yammacin kasar.
An rahoto cewa Darektan kwamitin ya kamanta Peter Obi da Azikiwe, Kwankwaso da Aminu Kano. Da irin haka ya faru a 1979, Shagari ne ya yi galaba.
Hasashen kwamitin shi ne Atiku za iyi nasara a duka bangarorin Arewa da Kudu maso kudu, Tinubu zai lashe wasu jihohin Arewa da na Yamma kurum.
A karshe dai, Momodu ya ce jam’iyyar APC ba za tayi nasara, ya kuma kara da cewa tunanin murdiya da Bola Tinubu yake yi ba zai yi aiki a zaben bana ba.
Osita Chidoka yana ganin nasarar PDP
A wani hasashe da Osita Chidoka ya yi, an ji labari ya nuna cewa Atiku Abubakar ya kama hanyar doke sauran ‘yan takara,ya zama Shugaban kasa a Mayu.
Osita Chidoka yake cewa PDP za ta samu kuri’u babu sosai a Oyo, Osun, da Ekiti, ya kuma ce za suu tashi da kuri’u masu tsoka a Anambra, Imo da Abia.
Asali: Legit.ng