2023: Tsoffin Yan Majalisa, Shugabannin Majalisa, Kwamishinoni Da Wasu Jiga-jigan PDP Sun Koma APC

2023: Tsoffin Yan Majalisa, Shugabannin Majalisa, Kwamishinoni Da Wasu Jiga-jigan PDP Sun Koma APC

  • Gabannin babban zaben 2023, jam'iyyar PDP ta yi babban rashi na wasu jiga-jiganta a jihar Delta
  • Tsoffin yan majalisa, shugabannin majalisa, kwamishinoni da wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa sun koma APC a jihar ta kudu
  • Dan takarar gwamnan APC a jihar, Sanata Ovie Omo-Agege ya kalubalanci takwaransa na PDP da ya fito su yi mahawara

Delta - Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa na 2023, manyan jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 26 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta, rahoton Thisday.

Masu sauya shekar sun hada da tsoffin mambobin majalisar wakilai, mamba a kwamitin amintattu na PDP da wani tsohon kwamishina tsoffin shugabannin majalisar jiha biyu, yan majalisar tarayya.

Cikin wadanda suka sauya shekar harda tsoffin kwamishinoni biyar da wasu jiga-jigan jam'iyyar adawar tare da magoya bayansu.

Kara karanta wannan

Atiku zai tashi a tutar babu a wata jihar da ya saka rai, jiga-jigan PDP sun bi Tinubu

PDP da APC
2023: Tsoffin Yan Majalisa, Shugabannin Majalisa, Kwamishinoni Da Wasu Jiga-jigan PDP Sun Koma APC Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jerin sunayen jiga-jigan PDP da suka koma APC a jihar Delta

Masu sauya shekar sune; Hon Mercy Almona Isei, tsohuwar kwamishina kuma tsohuwar mamba a majalisar wakilai ta kasa, Hon Daniel Reyenieju, tsohon dan majalisar wakilai, Hon Olisa Imegwu, tsohon kakakin majalisar Delta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran sune Hon Monday Igbuya, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Cif Judith Enamuotor, mamba a kwamitin amintattu na PDP kuma tsohon kwamishina, Hon Timi Tonye.

Sai kuma tsohon kwamishina kuma tsohon mamba, DTHA, Hon Evans Iwurie, tsohon kwamishinan raya birane da ci gaban matasa, Kwamrad Mike Akpobire, da kuma Cif Pius Ovbije tsohon kwamishinan DESOPADEC.

Ka fito mu yi muhawara, dan takarar gwamnan APC a Delta ya kalubalanci takwaransa na PDP

A halin da ake ciki, mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar gwamnan APC, Sanata Ovie Omo-Agege, ya kalubalanci dan takarar gwamnan PDP a jihar, Hon. Sheriff Oborevwori, da su yi mahawara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

Omo-Agege ya bukaci hakan ne da yake jawabi a garin Obinomba, karamar hukumar Ukwuani da ke jihar yayin da yake ci gaba da yakin neman zabe da tarbar wasu shugabannin PDP da suka dawo APC.

Ya caccaki Oborevwori kan rabewa da yake yi da ubangidansa a siyasa kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa, a kamfen dinsa.

Dan majalisar tarayyar ya kuma bukaci al'ummar jihar Delta da su matsa masa kan ya yi masu jawabi a budaddiyar muhawara wanda za a watsa a kasa.

Ya kuma kalubalanci Oborevwori da ya fadama mutanen Delta abun da ya yi a matsayinsa na kakakin majalisa mafi dadewa da kuma abun da zai yi idan aka zabe shi a matsayin gwamna a 2023, rahoton Leadership.

A wani labari na daban, mun ji cewa an kawo karshen yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihar Bauchi ba zato ba tsammani bayan daukewar na'urar sauti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng