Jigawa: Magoya Bayan PDP Sun Wanke Inda Tinubu Yayi Kamfen Tas da Ruwa

Jigawa: Magoya Bayan PDP Sun Wanke Inda Tinubu Yayi Kamfen Tas da Ruwa

  • Awanni kadan bayan zagayen APC da magoya bayan 'dan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, suka yi a Aminu Kano Triangle da ke Jigawa, jam'iyyar adawa ta wanke wurin tas
  • Wankin wurin yazo ne bayan magoya bayan jam'iyyar PDP sun zargi APC da kasancewa mai da kazanta, zubda jinanai da sauran munanan abubuwa a fadin kasar
  • A cewarsu, nasarar kammala zagayen ba tare da tangarda ba yazo ne saboda mulkin PDP ne ya samar da wurin kamfen da filin jirgin saman, kuma talakawa zasu tumbuke APC

Jigawa - Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar adawa na PDP sun wanke wurin da magoya bayan 'dan takarar shugaban kasa jam'iyyar APC, Bola Tinubu yayi zagaye a ranar Lahadi a jihar Jigawa.

Kamfen din Tinubu a Jigawa
Jigawa: Magoya Bayan PDP Sun Wanke Inda Tinubu Yayi Kamfen Tas da Ruwa. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

An gano yadda magoya bayan 'dan takarar shugaban kasar jam'iyya mai mulkin a ranar lahadi suka yi zagaye a Mallam Aminu Kano Triangle da ke jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Manyan Jihohi 2 da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun PDP da Dalili

Wankin wurin yazo bayan wasu awanni da 'dan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu yayi zagaye a ranar Lahadi, Premium Times ta rahoto.

Magoya bayan PDP tare da Umar Danjani - shugaban matasan PDP na kungiyar kamfen din Atiku Abubakar na PDP ya jagoranta, sun zargi magoya bayan APC na jihar da lalata wurin kamfen din da tsohon gwamna Sule Lamido ya gina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban matasan ya ce APC bata tabuka abun a zo a gani ba a jihar, inda ya zargi cewa, bayan mulkin PDP, garkuwa da mutane gami da neman kudin fansa da sauran munanan abubuwa suka zama ruwan dare a jihar.

Danjani ya ce, zagayen APC ya tafi lami lafiya ne saboda wurin zagayen da filin jirgin da mulkin PDP ta samar, inda ya bada tabbacin za su tumbuke APC daga madafun iko a zabe mai karatowa.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Ba A Ganin Osinbajo Wurin Kamfen Din Tinubu, APC

Danjani ya ce, taron wanke daudar an yi ne don wanke jinanan da suka zubar a rikicin manoma da makiyaya wanda mulkin APC ta gaza shawo kan shi.

"PDP ta fi karfi a Jigawa, jam'iyyar za ta dawo kan madafun iko bayan shekarun da aka gwada mulkin APC wanda ya gaza.
"Mun zo ne don wanke duk cutuka, mulkin kama karya, rashin tsaro, yunwa, talauci, rabe-raben kawuna da suka kawo nan, yayin da PDP ta shirya dawo da burin talakawa."

- A cewar Danjani.

Barin barin APC, daraktan kamfen din Tinubu ta gana da Atiku a Abuja

A wani labari na daban, Sanata Naja'atu Muhammad, tsohuwar daraktan kamfen din Bola Ahmed Tinubu a jihar Kano, ta gana da 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a Abuja.

Wannan na zuwa ne cikin sa'a 72 da ta bar jam'iyya mai mulki tare da cewa jam'iyyun siyasa basu da banbanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel