Sarkin Masarautar Dutse Jihar Jigawa Jigawa Yace Tinubu Nada Duk Wata Dama Ta Mulkar Nigeria

Sarkin Masarautar Dutse Jihar Jigawa Jigawa Yace Tinubu Nada Duk Wata Dama Ta Mulkar Nigeria

  • Sarkin ya marawa Tinubu baya ne sabida yace yana da hali mai kyau, kamar yadda abokinsa ya fada masa
  • Sarkin ya marawa Tinubu baya ne sabida shi mai neman na kansa ne a kowannen hali ko a ina
  • Sarkin yace kwarewarsa da gogewarsa tasa zai iya mulkar Nigeria, kamar yadda aka gani a jihar Lagos

Dutse - Mai martaba sarkin Dutse, Alh Nuhu Muhammad Sunusi ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC yana da duk abinda ake bukata wajen mulkar Nigeria

Sarkin gargajiyan ya alakanta hakan da abubuwan more kasa da Tinubun ya aiwatar a jiharsa ta Lagos.

Yan Takara
Sarkin Masarautar Dutse Jihar Jigawa Jigawa Yace Tinubu Nada Duk Wata Dama Ta Mulkar Nigeria Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya saki layin Tinubu? Gaskiya ta fito daga bakinsa, ya bayyana komai

Yayin da yake magana a karshen makon nan lokacin da Tinubun ya ziyarceshi a fadarsa, sarkin yace jam'iyyar ta hada kan yan arewa da yan kudu waje guda. Rahoton Daily Trust

Sarkin yace:

"Ina mutukar bibiyar aiyukanka, kuma ina tabbacin kai kadai ne zaka iya mulkar yan Nigeria"
"Nigeria tana tangal-tangal, amma yanzu ka hada kan arewa da kudu waje guda akarkashin yakin neman zabenka"
"Na halarci nadinka da aka yi na Jagaban Bargon, wanda marigayi sarkin Bargon ya nadaka wanda yake abokina ne kuma ya fada min halayyyarka"

Sannan sarkin ya ci gaba da cewa, kaje kasar Amurka, kayi karatu kamar dai ni, kuma kayi aiyuka masu yawa dan ka rayu a can, haka nima nayi wannan aiyukan

"kuma nima akawu ne kamar ka, kuma na karanta litttafanka wanda ka wallafa akan harkokin kudi da da kuma siyasa"

Jaridar The Cable tace dan takarar shugaban kasan na tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa, da dan takarar gwamnan jigawan da kuma dan takarar gwamnan jihar kano

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Tinubu ga Sarki

Tinubu yace ya yanke hukuncin ziyartar mai martaba sarkin ne a matsayinsa na uban kasa, kuma sun ziyarceshi dan neman tabarraki.

Ya tabbatarwa da sarkin cewa masu mukaman gargajiya zasu taru suga sun fitar da Nigeria daga cikin aiyukan da ake fama da ita.

Gwamnan jihar Jigawa yace godewa gwamnan kan irin tarbar da yayi musu da yan tawagarsa, yace sarkin ya girmamasu a matsayinsa na uban kasa.

Gwamnonn jam'iyyar APC shida ne da shugaban majalissar dattijai suka ziyarci fadar sarkin gami da yan majalissar wakilai na Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel