Shugaban Kasa a 2023: Lagas da Wasu Jihohi 4 da Buhari Zai Ziyarta Don Yi Wa Tinubu Kamfen
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yin duk abun da zai iya don mika mulkin kasar cikin nasara
- Yan makonni kafin zaben shugaban kasa na 2023, Buhari zai kai ziyarar aiki wasu jihohi a Najeriya da wata kasar waje
- Ana sa ran Shugaban kasar zai halarci gangamin kamfen din Bola Tinubu sannan zai kai ziyarar aiki Dakar, Senegal
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara wasu manyan jihohi a kasar don aiwatar da muhimman aiki.
Bashir Ahmad, mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwar zamani ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter.

Asali: Twitter
Buhari zai jagoranci yakin neman zaben APC a manyan jihohi biyar
A cewar hadimin Shugaban kasar, Buhari zai ziyarci wasu jihohi a Najeriya don jagorantar yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sannan zai kai ziyarar aiki wata kasar waje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Ahmad, ubangidan nasa zai ziyarci jihohi kamar haka:
1. Bauchi
2. Legas
3. Katsina
4. Kano
5. Jigawa
Sai kasar waje 1:
6. Dakar, Senegal.
Ahmad ya rubuta a shafin nasa:
“A yan kwanaki masu zuwa, Shugaban kasa @MBuhari zai kasancewa Bauchi don yiwa Asiwaju Tinubu kamfen; Lagas ziyarar aiki; Dakar, Senegal, taron kasa da kasa, Katsina, Kano da Jigawa, ziyarar aiki don kaddamar da wasu ayyuka na gwamnatocin tarayya da na jiha."
Jam'iyyar APC na hararar wasu jihohin PDP biyu gabannin zaben 2023
A wani labarin kuma, gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyun siyasa na ta gyara kwanjinsu na ganin sun yi nasarar lashe zaben.
Manyan jam'iyyun kasar guda biyu wato APC mai mulki da PDP mai adawa na ta kokarin tallata kansu da ganin sun sace zukata al'ummar kasar a zaben da za a yi a watan gobe.
A cikin haka ne, jam'iyyar APC ta shirya wasu dabaru na ganin ta kwato wasu jihohin PDP guda biyu ta hanyar tabbatar da ganin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga sahun masu yiwa Asiwaju Tinubu kamfen.
Jihohin sune Bauchi da Akwa Ibom kuma suna da matukar muhimmanci ga jam'iyyar mai mulki kasancewarsu masu albarkatun man fetur.
Asali: Legit.ng