Buhari Zai Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi

Buhari Zai Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi

  • Jihohin da ba jam'iyyar APC ce ke mulki ba, an shirya tun tuni cewa shugaba Muhammadu Buhari ne zai jagoranci yakin neman zabensu ko kaddamarwa
  • Ciki kuwa harda jihar Bauchi wanda Bala Muhammad ke a matsayin gwamnanta a karo na farko, kuma yake neman wa'adi na biyu
  • A kasa da awa 24 shugaba Buhari zai halarci garin na bauchi dan bawa dan takarar jam'iyyar APC tuta da kuma jagorantar nasarar jam'iyyar a jihar

Abuja - A gobe Litinin, Shugaba Muhammadu Buhari zai jagoranci yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa da na gwamna a jihar Bauchi.

A jaddawalin yakin neman zaben da shugababuharin zaiyi a karshen makon nan, ya nuna shugaban zai jagoranci yaki neman zabe a jihar Bauchi.

Kamar yadda aka tsara, Shugaba Muhammadu Buhari zai kasance a Bauchi da misalin karfe 8:30 zuwa 11:30 na safe wato awa uku kenan kacal.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Manyan Jihohi 2 da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun PDP da Dalili

Yakin neman zaben zai gudana ne da sassafe ba kaman yadda ake ganin na sauran jihohi ba, sabida uzirin shugaban na zuwa jihar Lagos dan ziyarar aiki ta kwana biyu.

Mai Buhari zai je yi jihar Lagos

Buhari zai kaddamar da wasu aiyuka da suka hada da, tashar jirgin ruwan Lekki, da tsarin sufurin kai da kai na hadin gwuiwa da gwamnatin tarayya da jihar Lagos da kuma wani kamfani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan Buhari zai kaddamar da aikin wani kamfani da zai ringa sarrafa shinkafa wanda yawanta yakai tan dubu 32 a awa daya wanda yake shine irinsa na duniya.

Buhari
Buhari Zai Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi
Asali: UGC

Ana sa ran zai bude sabon sufurin jirgin kasan jihar Lagos da kuma cibiyar da zata bunkasa al'ada da rayuwar yarabawa. Rahotan The Nation.

Sannan kuma daga nan shugaban zai wuce zuwa jihar Abia da Ogun a ranar Talata da Laraba.

Kara karanta wannan

Taron kamfen da rikicin PDP: Gwamnan PDP ba zai marabci Atiku a jiharsa ba bisa dalilai

Sannan kuma yan takarar jam'iyyar APC zasu kasance cikin matsin yakin neman zaben, dan zasu jagoranci jihar Benue da kuma Taraba

Yakin neman zaben dan takarar shugaban kasan a jam'iyyar APC zai gudana a Abuja babban birnin tarayya a ranar Juma'ar nan, sannan za'a kaddamar da bada shirin Tarakta ga manoma a Abujan.

Zuwa Yanzu

Kawo yanzu dai yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC da PDP sun karade rabin yawan jihohin Nigeria, inda dan takarar shugaban kasan PDP ya kamala da yankin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel