Gwamna Yahaya Bello Ya Musanta Rahoton Ya Janye Daga Goyon Bayan Tinubu

Gwamna Yahaya Bello Ya Musanta Rahoton Ya Janye Daga Goyon Bayan Tinubu

  • Gwamnan jihar Kogi kuma Koodinetan matasa ya musanta rahoton da ke cewa ya tsame kansa daga jirgin yakin zaben Tinubu
  • Alhaji Yahaya Bello ta tabbbatarwa yan Najeriya cewa kauna da goyon bayan da yake wa Tinubu da Shettima na nan 100%
  • Wannan na zuwa ne kwana ɗaya tal bayan Daraktan sashi guda a kamfen Tinubu ta yi murabus daga mukaminta

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ya fice daga jirgin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC.

Gwamnan ya ƙaryata raɗe-radin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook ranar Lahadi 22 ga watan Janairu, 2023.

Bola Tinubu da Yahaya Bello.
Gwamna Yahaya Bello Ya Musanta Rahoton Ya Janye Daga Goyon Bayan Tinubu Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Gwamna Bello yace goyon bayan da yake wa Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima bai canza ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Janye Daga Goyon Bayan Tinubu a Zaben 2023

Wasu rahotanni da kafafen watsa labarai da dama suka wallafa sun nuna cewa Yahaya Bello ya tsame kansa daga kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce wannan rigima da ta kai ga janyewar Yahaya Bello ba zata rasa nasaba a shirye-shiryen babban zaben gwamnan jihar da ke tunkarowa ba a watan Nuwamba.

Ina nan daram a layin Tinubu - Yahaya Bello

Da yake karyata raɗe-raɗin a shafinsa, Yahaya Bello ya ce:

"Babu tantama goyon bayan da nake wa Tinubu/Shettima na nan 100 bisa 100, Allah ya albarkaci APC, Allah ya albakaci tarayyan Najeriya."

Wannan ci gaban ya zo ne awanni 24 bayan babbar jigo a kwamitin kamfen shugaban kasa na jam'iyyar APC ta yi murabus.

Naja’atu Muhammad, wacce ke rike da muƙamin Darakta a tawagar kamfen Tinubu ta sauka daga kan muƙaminta ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wasu Jiga-Jigan APC Sun Cinye Kudin Ralin Bola Tinubu a Jihar Arewa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jirgin yakin ɗan takarar APC ya gamu da wannan babban tasgaro ne saura wata ɗaya da yan kwanaki babban zabe.

A wani labarin kuma Atiku ya bayyana yadda Buhari da APC suka yaudari mutanen Neja da arewa a zaben 2019

Mai neman shugaban ƙasa a PDP ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya cuci mutanen jihar Neja domin ya samu kuri'unsu ya zarce zango na biyu kan Mulki a 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya ƙara da cewa gwamnatin APC ta zo da batun canji amma sai ga shi canjin ya zo ba yadda mutane suka yi tsammani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262