Wasu Kusoshin APC Sun Yi Sama da Faɗi da Kudin Shirya Ralin Tinubu a Taraba

Wasu Kusoshin APC Sun Yi Sama da Faɗi da Kudin Shirya Ralin Tinubu a Taraba

  • An zargi wasu masu faɗa aji a siyasar jihar Taraba da yin sama da faɗi da kudaden Ralin Bola Tinubu/Shettima
  • A ranar 20 ga watan Janairu aka shirya gudanar da Rali a jihar amma APC ta sanar da ɗage zuwa jihar sai nan gaba
  • Kodinetan shiyyar kudancin Taraba yace har yanzun APC ba ta da ɗan takarar gwamna saboda batun na gaban Kotu

Taraba - Ko-odinetan kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima na kudancin jihar Taraba, Chief David Sabo Kente, ya yi ikirarin wasu 'yan siyasa sun cinye kuɗin kamfe.

Ya ce kuɗin da aka ware domin shirya ralin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC a Taraba, wasu sun karkatar dasu zuwa Aljihunansu domin kawo cikas ga jam'iya.

Bola Tinubu.
Wasu Kusoshin APC Sun Yi Sama da Faɗi da Kudin Shirya Ralin Tinubu a Taraba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kente ya yi wannna zargin ne a wurin Ralin da aka shriya na shiryyar Wukari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motar Ɗan Takarar Gwamna Wuta

A cewarsa wasu daga cikin masu ruwa da tsakin jam'iyya ne suka tilasta wa kansu haɗa kudi domin tabbatar da Ralin shiyyar ya gudana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa APC ta ɗage ralin Tinubu a Taraba?

Kodinetan ya bayyana cewa an ɗage babban Ralin Tinubu/Shettima na jihar Taraba ne saboda har yanzu APC ba ta da ɗan takarar gwamna a jihar.

Yace tanar 20 ga watan Janairu, 2023 aka tsara zuwan Tinubu amma tilas aka ɗaga saboda shari'ar dake gaban Kotun koli kan sahihin ɗan takarar gwamna.

"Mu muka haɗa kudi daga Aljihunanmu domin shriya wannan ralin saboda kuɗin da aka ware wa Ralin ɗan takarar shugaban kasa wasu sun hamdame su."
"Muna kaunar jam'iyarmu kuma a shirye muke mu yi duk mai yuwuwa domin ganin ta kai ga nasara a zabe."

- Chief Kente.

Bayan haka, Basaraken Wukari watau Aku Uka na Wukari, Manu Ishaku Adda Ali, ya yi kira ga 'yan siyasa da su rika nuna halayya mai kyau da zata kara haɗa kan juna maimakon ta da rigima da ruguza wasu.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Ruɓe, An Bayyana Wanda Ya Kamata Kwankwaso Ya Janye Wa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Basaraken ya yaba wa Chief David Sabo Kante bisa namijin kokarinsa na jan mutane a jiki a dukkanin harkokin siyasarsa, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Rikicin PDP: Kar ku zargi G-5 idan aka gaza samun masalaha - Ortom

A wani labarin kuma Gwamna Ortom ya gargadi shugabannin PDP kan rikon sakainar kashin da suke wa batun sulhu da G-5

Ortom, daya daga cikin jagororin tawagar gaskiya, yace kar a zargi kowa a zargi PDP idan har G-5 ta rufe kofar neman maslha da tsagin su Atiku.

Bayan haka gwamnan ya bayyana dan takarar da ya kwanta masa a rai duba da yanayin da Najeriya ta tsinci kanta a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel