PDP Ta Jawo Danyen Rikici, Gwamna Wike Yana Barazanar Kai Jam’iyyar Zuwa Kotu
- Gwamna Nyesom Wike ya maidawa majalisar NWC martani saboda dakatar da wasu ‘Yan PDP
- A ra’ayin Nyesom Wike, shugabannin jam’iyyar PDP sun saba doka, kuma zai kai kara a gaban kotu
- Gwamnan na Ribas yace dakatar da ‘yan jam’iyya ba zai taimakawa Iyorchia Ayu da mutanensa ba
Rivers - Gwamna Nyesom Wike ya soki matsayar da uwar jam’iyya ta dauka a karshen makon nan na rusa shugabannin PDP na reshen Ekiti.
Daily Trust ta rahoto Mai girma Nyesom Wike yana zargin majalisar Iyorchia Ayu da yin karfa-karfa, har kuma ya nuna zai kai maganar zuwa kotu.
Gwamnan na jihar Ribas ya kalubalanci shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu da ya dakatar da shi ko daya daga cikin Gwamnonin da ke tafiyar G5.
Wike ya tofa albarkacin bakinsa ne lokacin kaddamar da yakin neman zaben PDP a garin Bori da ke karamar hukumar Khana ta Ribas a ranar Asabar.
Magana za ta iya kai kotu
Gwamnan ya nuna zai kai karar shugabannin jam’iyyar adawar a kotu, domin jin ko uwar jam’iyya na da hurumin sauke shugabanninta na reshen Ekiti.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
The Nation Gwamnan yana cewa ya kamata majalisar NWC ta bar doka da tsarin mulki suyi aiki.
Maganar da Nyesom Wike ya yi
"Bari in yi amfani da wannan daman in fadawa Iyorchia Ayu da mutanensa rusa shugabannin jihar Ekiti ba zai taimaka maka ta kowace irin hanya ba.
Dakatar da mutane sam ba zai taimake ba. An ja layin yaki da kyau. Yanzu maganar da nake yi, za mu yi duk abin da za mu iya wajen neman hakki a doka.
Za mu yi bakin kokarinmu na kalubalantar duk wani matakin da muka san ya sabawa doka."
- Gwamna Nyesom Wike
A zabi 'Yan PDP - Wike
Da yake jawabi a jiya, Wike ya ce dakatarwar da jam’iyyarsa tayi wa wasu ‘ya ‘yanta shirme ne kurum, ya ce ba a isa ayi wa wani barazana a PDP ba.
A jawabin da ya yi, Gwamnan ya tabbatar ya yi kira ga mutanen Khana da su zabi Siminialayi Fubara da duk ‘yan takaran majalisar PDP a zaben bana.
Rikicin LP a Kano
Dazu rahoto ya zo cewa saboda wani sabani jam’iyyar adawa ta LP ta shiga rudani a gabar yawon yakin neman zaben shugaban kasa da za ayi a jihar Kano.
Bashir Bashir, Mohammed Zarewa, Balarabe Wakili da Idris Dambazau za su kauracewa kamfe a dalilin jawo wasu cikin kwamitin yakin zabe.
Asali: Legit.ng