Ana Tsaka Da Kamfe Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Fadi Ya Mutu

Ana Tsaka Da Kamfe Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Fadi Ya Mutu

  • Yayin gangamin zaben dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, shugaban jam'iyyar ya kwanta dama
  • Dama wasu rahotannni na cewa shugaban jam'iyyar na fama da wasta cuta wadda take da alaka da numfashi
  • Har kawo zuwa yanzu jam'iyyar bata fitar da wata sanarwa kan rasa ran shugaban jam'iyyar ba

Enugu - Shugaban riko na jam'iyyar PDP, a karamar hukumar mulki ta jihar Udi dake jihar Enugu, SKB Ogbuagu ya rasa ransa

Ogbuagu ya fadi sabe-shabe a lokacin da ake tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar na dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, wanda aka gudanar a karamar hukumar Ezeagu ta jihar

Yadda abun ya faru

Wata majiya da ta shedawa jaridar The Punch, cewa lokacin da aka tashi daga wajen mitin din kowa na tafiya wajen karbar abinci shine abinda da ya sameshi ya sameshi na rasa ransa

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Atiku: Jam'iyyar PDP ta yiwa APC raddi

Shugaban rikon kwaryar wanda ake zargin yana dauke da Asma, wanda aka garzaya da shi asibiti mafi kusa wanda kuma anan ne yace ga garinku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar PDP
Ana Tsaka Da Kamfe Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Fadi Ya Mutu Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wannan lamarin dai ya faru ne a ranar Alhamis din nan data gabata, amma har yanzu jam'iyyar PDP bata fitar da wata sanarwa makamancin wannan ba.

Mai jam'iyya tace

Duk wani yunkuri da akai najin bakin shugaban jam'iyyar na jihar abin ya ci tura, bai daga waya ba, bai dawo da sakon kar ta kwannan da aka tura masa ba.

Daily Post ta rawaito cewa har mutuwar SKB Ogbuagu shine shugaban jam'iyyar PDP na riko na karamar hukumar sabida sabanin da ake samu a jam'iyyar a karamar hukumar Udi ta jihar Enugu

Hukumar zaben Nigeria ta fitar da jaddawalin yan takarar da zasu fafata a zaben shugaban kasa

Kara karanta wannan

Ba'a Ga Keyar Dan Takarar Jam'iyyar ADP Na Gwamna A JIhar Kaduna A Wajen Muhawara Da BBC Hausa Ta Shirya

Yan takarar goma sha takwas ne zasu fafata a zaben shugaban kasa da za'a gudanar a ranar 25 ga watan Fabairun shekarar da muke ciki.

Yan takarar wanda suka fito daga jam'iyyu goma sha takwas sun daura damar yadda zasu dare kujarar shugaban cin kasa a wannan shekarar.

Daga cikin manyan yan takarar da zasu fafata akwai Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, wanda Kashim Shettima ke masa takarar mataimakin shugaban kasa,

Akwai Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa na jam'iyyar PDP, da kuma Peter Obi da Datti Babba Ahmed na jam'iyyar LP, Sai Rabi'u Kwankwaso da Pastor Idohosa na jam'iyyar NNPP, da kuma Major Hamza Almustapha mai ritaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel