Gwamnan Anambra Ya Tona Asirin Abin da Peter Obi Ya yi wa LP a Lokacin Mulkinsa
- Jam’iyyar LP tana zargin Gwamnatin Charles Chukwuma Soludo da hana sun yi kamfe a Anambra
- Mai girma Charles Soludo ya kare kan shi, ya ce ya kyale LP tayi kamfe ba tare da biyan kudi ba
- Mutanen Peter Obi su na korafin ana cire masu fastoci, Gwamnan Anambra ya ce doka aka saba
Anambra - Charles Chukwuma Soludo mai mulkin jihar Anambra ya ce a lokacin tsohon Gwamna Peter Obi, ba a ba jam’iyyar LP damar yakin zabe ba.
Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya jefi Peter Obi da wannan zargi ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.
Charles Chukwuma Soludo ya yi wannan magana ne domin maida martani ga shugabannin LP na Anambra da ke zarginsa da hana su yin kamfe.
Mai girma Gwamnan ya shaidawa tashar Channel a tattaunawar da aka yi da shi cewa sau biyu gwamnatinsa ta na amincewa Obi yin kamfe a jihar.
Farfesa Soludo yake cewa ba zai bata lokacinsa yana magana kan babatun ‘yan adawa ba domin tuni hukumomin da ke da alhaki sun yi karin bayani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Amma abin da yake shi ne sau biyu ina ba ‘dan takaran shugaban kasa na LP damar amfani da kayan gwamnati domin yin kamfe ba tare da karbar sisi ba.
Babu wanda ya yi wannan, bai yi haka a lokacin da yake mulki ba. Bai kyale jam’iyyar LP da yanzu yake cikinta su yi kamfe da kyau a jihar Anambra ba.
Shi (Peter Obi) ya hana su (jam’iyyar LP) amfani da dakin taron da suka biya kudi a kai."
- Charles Chukwuma Soludo
Doka tana aiki a kan kowa
The Cable ta rahoto Gwamnan yana cewa idan jam’iyya ta saba dokar Anambra, ta daura allon takara ba tare da biyan kudi ba, hukuma za ta cire allon.
Tsohon gwamnan na CBN ya gaskata abin da yake fada da cewa an cire faston wani mai neman takarar majalisar tarayya a APGA – jam’iyya mai mulki.
Mubaya'ar Obasanjo ga LP
A wani rahoto, an ji labari Olusegun Obasanjo ya yi karin bayani a game da ra’ayinsa a kan masu neman mulki a zaben 2023, ya kare kan shi daga suka.
Obasanjo yake cewa Najeriya na bukatar mai halin kwarai ne ya jagorance ta kuma ya ce bai taba fadawa ‘Yan Najeriya cewa ya yi wa Peter Obi mubaya’a ba.
Asali: Legit.ng