Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Ce Akwai Yiwuwar Peter Obi Zai Ci Zabe A Jiharsa

Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Ce Akwai Yiwuwar Peter Obi Zai Ci Zabe A Jiharsa

  • Farfesa Chukwuma Soludo, gwamnan jihar Anambra ya ce yana kyautata zaton Peter Obi dan takarar Jam'iyyar Labour zai ci zabe a jiharsa
  • Soludo ya kuma ce yana yi wa Obi fatan alheri duk da cewa shima dan jam'iyyarsu na APGA yana takarar shugaban kasar
  • Amma, duk da hakan shugaban na jam'iyyar APGA na kasa ya ce baya tunanin Obi zai iya yin nasarar lashe babban zaben baki daya

Farfesa Chukwuma Soludo gwamnan jihar Anambra ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, zai iya cin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, Vanguard ta rahoto.

Soludo ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels TV, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gwamnan Anambra Ya Tona Asirin Abin da Peter Obi Ya yi wa LP a Lokacin Mulkinsa

Soludo da Obi
Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Ce Akwai Yiwuwar Peter Obi Zai Ci Zabe A Jiharsa. Hoto: Vangaurd
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ina yi wa Peter Obi fatan alheri. Ya tafi ya fafata da sauran, "Mu a (APGA) mu ma muna takara a zaben. Muna da namu dan takarar (Peter Umeadi), wanda shima dan mu ne, shima daga jihar Anambra, shima zai yi nasa, zai samu kuri'unsa."

Gwamnan ya yi magana kan rubutun da ya fitar a Nuwamban 2022, inda ya ce ta yi wu Obi ya ci zabe a Anambra amma ba zai iya cin zaben a kasa ba.

Ya ce:

"A wannan rubutun, na ma ce ta yi wu Peter Obi zai iya cin zabe a jihar Anambra. Na fada hakan."

Amma, Soludo ya ce baya tunanin cewa Obi zai iya cin babban zaben da za a yi a watan Fabarairu.

Gwamna Soludo, wanda shine sabon shugaban jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) na kasa ya ce ya bawa Obi dukkan goyon bayan da ya ke bukata a matsayinsa na tsohon gwamna, wanda ya mulki jihar daga 2006 zuwa 2014.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Za Su Yi Alfahari da Kasancewarsu Yan Najeriya Idan Na Gaje Buhari, Peter Obi

Gwamnan ya ce yana yi wa dukkan jam'iyyun siyasar adalci kuma bai hana kowa wurin yin kamfen ba.

Idan za iya tunawa Mr Soludo da Obi sunyi jayayya kan tattalin arziki da saka hannun jari a jihar Anambra.

Gwamnan na Anambra, Soludo ya ce hannun jarin da Obi ya bari kusan ba su da amfani.

Malamin addini ya bayyana abin da zai faru a zaben gwamnan Abia, Katsina da Taraba

Kun ji cewa Elijah Ayodele, fitaccen malamin addini a Najeriya ya ce Alex Otti na jam'iyyar LP da Enyinnaya Nwafor na jam'iyyar YPP za su iya cin zaben gwamna a Anambra.

A cewarsa, muddin sun yi irin shirin da ya dace toh za su iya yin nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel