2023: Ko Sama Ko Kasa Ba a Ga Gwamna Makinde a Wajen Kamfen Din Atiku Ba

2023: Ko Sama Ko Kasa Ba a Ga Gwamna Makinde a Wajen Kamfen Din Atiku Ba

  • Ba a ga Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ba a wajen gangamin kamfen din Atiku Abubakar da ke gudana a garin Ibadan
  • A yau Alhamis, 19 ga watan Janairu ne aka kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na PDP a zaben 2023 a filin taro na Mapo da ke Ibadan, jihar Oyo
  • Sai dai, hasashe sun nuna cewa an yi sulhu tsakanin Atiku da Makinde domin magoya bayansa sun bukaci a zabi gwamnan na Oyo a karo na biyu a zabe mai zuwa

Oyo - Rahotanni sun kawo cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, bai halarci gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ya gudana a babban dakin taro na Mapo da ke garin Ibadan ba.

Sai dai kuma, manyan jiga-jigan PDP a jihar sun halarci gangamin inda manyan magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar, suka bukaci mambobin jam'iyyar da magoya baya a jihar su zabi Gwamna Makinde a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

Gangamin kamfen
2023: Ko Sama Ko Kasa Ba a Ga Gwamna Makinde a Wajen Kamfen Din Atiku Ba Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Gangamin na gudana ne a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo a yau Alhamis, 19 ga watan Janairu.

Atiku ya samu rakiyar gwamnan jihar Delta kuma abokin tarakararsa, Ifeanyi Okowa, Gwamna Ademola Adeleke, Gwamna Godwin Obaseki da Gwamna Aminu Tambuwal, rahoton Within Nigeria.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanayin yadda gangamin ke gudana a Ibadan ya nuna alamun cewa watakila Atiku da Makinde sun sulhunta tsakaninsu a bayan fage domin cimma alkibla guda gabannin babban zaben kasar mai zuwa a watan gobe, jaridar Leadership ta rahoto.

An magance banbancin da ke tsakanin Atiku da Makinde?

Yayin da gangamin kamfen din ke gudana, wadanda suka yi jawabi zuwa yanzu sun hada da uban taro, Sanata Dino Melaye, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Kara karanta wannan

Taron kamfen da rikicin PDP: Gwamnan PDP ba zai marabci Atiku a jiharsa ba bisa dalilai

Hakazalika uwargidar dan takarar shugaban kasa, Hajiya Amina Titi Atiku Abubakar da sauransu sun yi jawabi, kuma duk sun ce an magance banbancin da ke tsakanin Atiku da Makinde, inda suka bukaci mambobi da magoya bayan jam'iyyar su sake zabar Makinde.

Makinde da gwamnonin G-5 na rigima da Atiku kan Ayu

Ku tuna cewa Makinde na daya daga cikin fusatattun gwamnonin PDP biyar da ake yiwa lakabi da G-5 ko 'Integrity Group', wadanda basa ga maciji da shugabancin jam'iyyar saboda ci gaba da kasancewar Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.

Sun ce sai dai Ayu ya sauka wani dan kudu ya hau idan ba haka ba, ba za su yi wa Atiku kamfen ba domin a cewarsu babu yadda za a yi yan arewa su mamaye duk wasu mukamai na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng