Dan Takarar Shugaban Kasa a PDP, Atiku Abubakar, Ya Dira Ibadan Kamfe
- Jirgin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sauka a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
- Tun a filin jirgi aka samu matsala sakamakon rashin ganin gwamna Seyi Makinde a cikin wadanda suka je tarban Atiku
- Gwamna Makinde na daya daga cikin gwamnonin G-5 da suka ja daga da tsagin shugabancin PDP tun bayan zabe
Ibadan, Oyo - Mai neman zama shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wazirin Adamawa ya dira Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Atiku ya sauka a birnin da misalin karfe 12:00 na tsakar ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu 2023 domin halartar Ralin kamfen shugaban ƙasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya isa ne tare da rakiya mambobin kwamitin ayyuka na PDP ta kasa da tawagar kwamitin kamfen Atiku/Okowa.
Atiku ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa, "Yanzun nan na sauka a Ibadan domin abinda aka yi alkawari zama Ralin kamfe mai dumbin tarihi."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tawagar yakin neman zaben shugaban kasa ya samu tarba hannu mai kyau daga shugabanni da kuma mambobin jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Oyo.
Har yanzun PDP na cikin matsala
Sai dai zuwan Atiku ya kara tabbatar da akwai matsala a PDP har yanzun saboda gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, mamba a jam'iyyar, bai je wurin taro ɗan takarar ba a Filin jirgi.
Gwamna Makinde na ɗaya daga cikin gwamnonin tawagar G-5 kuma suna kiransa da matashin gwamnan tawagar gaskiya (G-5).
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa har yanzun ba'a ga maciji tsakanin tsagin G-5 karkashin jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da kuma shugabancin PDP.
Fusatattun gwamnonin sun lashi takobin ba zasu shiga tawagar tallata Atiku ba har sai shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus an ɗora dan kudu.
A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya ta yi watsi da karar da aka shigar da Tinubu kan hada takara Musulmi da Musulmi
Lauya mazaunin Abuja, Osigwe Momoh ne ya shigar da karar inda ya nemi kotun ta dakatar INEC daga amincewa APC ta shiga zaben watan Fabrairu.
A cewar Lauyan matakin ya saba wa kundin tsarin Mulkin Najeriya kuma ya yi karan tsaye ga sashi na 14, 15 Da 224 a kwansutushin ɗin Najeriya 1999.
Asali: Legit.ng