Zaben 2023: NRM Ta Maka Peter Obi A Kotu Kan Zargin Mallakar Takardun Izinin Zama Dan Kasashe Biyu

Zaben 2023: NRM Ta Maka Peter Obi A Kotu Kan Zargin Mallakar Takardun Izinin Zama Dan Kasashe Biyu

  • Wata kungiya ta maka Peter Obi a kotu kan ikirarin cewa dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour dan kasar Amurka ne
  • An saka INEC da jam'iyyar Labour a karar da aka shigar a babban kotun tarayya a kotun Najeriya, Abuja
  • A watan Oktoban 2022, Magajin garin Dallas ya karrama Obi da izinin zama dan kasa bisa jagorancinsa mai kyau

FCT, Abuja - Kungiyar National Rescue Movement, NRM, ta kai karar jam'iyyar Labour, LP, da dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi, a kotu kan zarginsa da mallakar izinin zama dan kasa guda biyu.

A karar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1842/2022 a babban kotun tarayya, wanda ya shigar da karar ya zargiObi da mallakar izinin zama a Dallas, Texas, kasar Amurka wanda hakan ya ci karo da sashi na 1 da 137 na kundin tsarin Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai Ƙura: “Ba a Gina Makarantar da Tinubu Yake Ikirarin Ya Yi Karatun Boko ba”

Peter Obi
Zaben 2023: NRM Ta Maka Peter Obi A Kotu Kan Zargin Mallakar Takardun Izinin Zama Dan Kasashe Biyu. Hoto: @PeterObi
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wadanda aka yi karar suna hukumar INEC, Peter Obi da jam'iyyar Labour.

Wanda ya shigar da karar yana fata kotu ta haramtawa Obi shiga takarar shugabancin kasa kan saba kundin tsarin kasa na 1999.

NRM kuma ta bukaci kotu ta bada umurnin hana hukumar zabe mai zaman kanta INEC amincewa ko bawa Obi wasu alfarma na tsayawa a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Don gabatar da hujjarta, kungiyar ta gabatar da hoto da bidiyo da ke nuna lokacin da aka mika wa Obi satifiket din zama dan Dallas.

Mai shari'a Inyang Edem Ekwo gargadi mai shigar da karar kan kin gabatar da takardun tuhumar ga wadanda aka yi karar, ya kuma saka ranar Juma'a 10 ga watan Fabrairu don sauraron karar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

Ekwo ya kuma yi barazanar fatali da karar idan wanda ya yi karar ya gaza bawa wadanda aka yi karar takardar shigar da su kara kafin ranar da aka zaba don fara sauraron karar.

Tafiyar Peter Obi ta samu kwarin gwiwa a Kaduna yayin da mataimakin kakakin majalisar jiha da mamba suka koma LP

A wani rahoton, kun ji cewa Isaac Auta Zankai, mataimakin kakakin majalisar jihar Kaduna da Suleiman Dabo mai wakiltar Zaria sun sauya sheka daga APC zuwa Jam'iyyar Labour.

Umar Farouk Ibrahim, sakataren jam'iyyar LP na kasa kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna na LP ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da mambobin kwamitin kamfen din gwamna tare da gabatar da manufofinsu a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel