Uwargidar Tinubu Ta Bayyana Yadda Suke Rayuwa a Gida Duk da Bambancin Addininsu
- Jagororin mata na jam’iyyar APC sun halarci taron yakin neman zaben da aka shirya a Owerri
- Oluremi Tinubu ta jero halayen Asiwaju Bola Tinubu na kwarai, ta roki ‘Yan Najeriya su zabe shi
- Sanata Oluremi Tinubu ta ce mijinta bai matsa mata wajen addininta ba, sai dai ma ya taimake ta
Lagos - Matar ‘dan takaran APC a zaben shugabancin Najeriya na 2023, Oluremi Tinubu ta yabi halin mai gidan na ta watau Asiwaju Bola Tinubu.
Vanguard ta fitar da rahoto cewa Sanata Oluremi Tinubu tayi kira ga al’ummar Najeriya su zabi mijinta domin bai da matsin lamba a harkar addini.
‘Yar siyasar ta shaidawa jama’a cewa jam’iyyar APC za ta cika duka alkawuran da ta dauka.
Remi Tinubu mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawa tun 2011 tayi wannan kira ne a taron kamfe da matan jam'iyyar APC suka shirya a jihar Imo.
Matan APC sun je kasar Ibo
Pulse ta ce kwamitin mata na yakin neman zaben Tinubu/Shettima a 2023 ya yi kamfe a filin wasan Rear Admiral Ndubuisi Kanu da ke garin Owerri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu tayi amfani da wannan dama, ta shaidawa mutanen Kudu maso gabas cewa mai gidanta zai yi wa kowa adalci idan mulkinsu ya fada a hannunsa.
Sanatar ta ce akwai bukatar a samu hadin-kai a Najeriya, saboda haka ne ta ke fada cewa tun da take, mijinta bai taba hana ta ‘yancin yin addinin ta ba.
Tinubu ya kafa mutane barkatai - Remi
Ko da Oluremi Tinubu kirista ce wanda ta kai matsayin babbar Fasto a coci, Bola Tinubu musulmi ne, kuma a haka suke rayuwa ba tare da matsala ba.
A cewar ‘yar majalisar, mijinta mai neman zama shugaban kasa ya taimaka mata wajen zama Fasto, haka kuma ya taimaki wasu mutanen a kasar nan.
“Za mu cika duka alkawuran da muka yi wa ‘Yan Najeriya har da kari. Ni fasto ce kuma limamiya a coci.
Kuma mai gidana ne ya rika ba ni goyon baya a addini na. Najeriya ta fi karfin batun addini ko kabilanci."
- Oluremi Tinubu
A gaban dinbin jagororin mata na APC da suka halarci taron, Remi Tinubu ta ce suna kaunar Ibo kuma gwamnatin Tinubu za ta dama da matan bangaren.
Kwankwaso a Chatham House
A yau labari ya zo cewa ‘Dan takaran NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi jawabi a dakin taro na Chatham House a Birtaniya.
‘Dan takaran ya ce zai iya fasa takara muddin a cikin masu neman shugabanci, akwai wani wanda ya fi shi, hakan na nuna bai da nufin fasa takara.
Asali: Legit.ng