Kar Ku Yarda da Mijina Idan Ya Gaza Kawo Sauyi a Shekara Hudun Farko, Matar Tinubu

Kar Ku Yarda da Mijina Idan Ya Gaza Kawo Sauyi a Shekara Hudun Farko, Matar Tinubu

  • Matar dan takarar shugaban kasa ta yi kira ga yan Najeriya su kayar da Tinubu idan har ya gaza aiki a zangon mulki na farko
  • Sanata Oluremi Tinubu ta ziyarci jihar Imo a ci gaba da yakin neman zaben Tinubu/Shettima na mata
  • Matar dan takaran ta kara bayani kan tikitin musulmi da Musulmi da har yau wasu ke suka a Najeriya

Imo - Matar dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Oluremi Tinubu, ta shawarci 'yan Najeriya su fatattaki Mijinta daga gadon mulki bayan shekaru hudu idan har aka zabe shi bai yi abinda ya dace ba.

Matar Tinubu ta yi wannan furuci ne a Ralin mata na tallata Tinubu/Shettima a shiyyar kudu maso gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Oluremi Tinubu.
Kar Ku Yarda da Mijina Idan Ya Gaza Kawo Sauyi a Shekara Hudun Farko, Matar Tinubu Hoto: Dailytrust
Asali: UGC
"Mu jingine batun addini a gefe, ni kirista ce shin kun taba tunanin watarana za'a jaraba tikitin Kirista da Kirista? Wai me asalin zancen ne, mun taɓa jaraba Musulmi da Musulmi to ku bari mu ƙara jaraba wannan."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

"Kuma bayan shekaru hudu, idan har ba su kawo sauyi mai kyau ba, zaku iya canza su daga kan mulki," inji mai dakin Tinubu, kamar tadda Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatar ta bayyana cewa bai kamata a zaben Najeriya a tsaya ana kace-kace kan imanin mutane ba, kamata ya yi mutane su natsu su ɗauki dan takara mai tsoron Allah.

Ta ci gaba da cewa:

"Idan kuka samu mutum mai tsoron Allah, ba wai Kirista, Musulmi ko Katolika ba, mai tsoron Allah. Idan mai tsoron Allah ne a gadon mulki zai muku abinda ya dace."

Tinubu zai ja mata a jiki idan ya ci zabe - Oluremi

Oluremi Tinubu, wacce ta bayyana cewa ta yi aiki a matsayin matar gwamna da Sanata, ta tabbatarwa mata cewa zasu samu gurbi mai tsoka a gwamnatin Tinubu da Shettima.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

"Wannan lokaci ne na yi wa Najeriya aiki babu zancen wasa. Batun mata, zamu tuna da ku kuma ika tabbatar masu da cewa Asiwaju zai tuna da ku. Tinubu da Shettima suna da kunshi na musamman ga matasa."

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya bayyana matakin da suke na zabar wanda zasu marawa baya a zaben 2023

Wike, jagoran gwamnonin tawagar gaskiya da ake kira G-5 ya raba gari da tsagin Atiku ne saboda kafa sharadin shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya yi murabus, ɗan kudu ya hau.

Gwamnan yace abun sha'awa da babban zabe mai zuwa shi ne babu kofar da jami'an tsaro zasu yi magudi ko su ba mutane tsoro a sauya sakamakon zaben,

Asali: Legit.ng

Online view pixel