Kwankwaso Ya Yi Maganar Janye Takara, Ya Fadi Abin da Zai Sa Ya Hakura da Neman Mulki
- Da zarar an samu wanda ya fi Rabiu Musa Kwankwaso cancanta da mulki, ‘dan takaran zai janye
- ‘Dan takaran shugaban kasa a NNPP ya ce zai ajiye burinsa idan aka fito da ‘dan takaran da ya fi shi
- Kwankwaso ya bayyana wannan sa’ilin da ya yi wa Duniya jawabi a dakin taron Chatham House
London - Idan har ta kama, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna a shirye yake ya janye takarar da yake yi na zama shugaban Najeriya a inuwar NNPP.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana wannan ne a lokacin da ya jero manufofi da muradunsa a dakin taro na Chatham House da ke Birtaniya.
Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Laraba, ;dan takaran shugaban kasar na NNPP ya ce zai hakura da takararsa idan ya ga wanda ya fi shi cancanta.
Har zuwa yanzu tsohon Gwamnan na Kano yana ganin ya fi duk abokan gwabzawar a zaben 2023 dacewa, hakan ya nufin ba zai fasa shiga filin zabe ba.
Akwai aiki a gaban NNPP
Kwankwaso zai fuskanci Bola Tinubu da yake takara a jam’iyya mai mulki ta APC, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi a jam’iyyar LP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A jawabin da ya yi a dakin taron da ke kasar Ingila, Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan takaran ya yi magana a kaikaice a game da wasu 'yan takaran.
Sanata Kwankwaso ya yi bayanin yadda ya so a ce sun hada-kai da Obi, amma lamarin ya faskara saboda jam’iyyar LP ta biyewa zugan jama'a.
Ayyukan da Kwankwaso zai yi a mulki
A game da ayyukan da zai yi idan ya ci zaben bana, jaridar ta rahoto Kwankwaso yana cewa zai farfado da tattalin arziki ta hanyar jawo hannun jari.
‘Dan takaran ya ce zai yaki talauci da rashin ilmin zamani da ake fama da shi a Arewa, Kwankwaso ya yi shekaru takwas yana gwamna a yankin.
A lokacin da yake Gwamna a Kano, Kwankwaso ya ce ya gina dakunan karatu fiye da 500, ya ce idan ya karbi shugabancin Najeriya, zai farfado da ilmi.
Har ila yau, Channels ta rahoto tsohon Ministan tsaron yana cewa zai dauki mutane a aikin damara, wanda hakan zai taimaka wajen rage ayyukan yi a Najeriya.
'Dan takaran PDP a Ekiti
A jiya rahoto ya zo cewa Atiku Abubakar ya je kamfe a Ekiti, amma ‘yan takara da Shugabanni Jam’iyyar PDP kusan 40 sun yi watsi da 'dan takaran.
Duk da haka taron Jam’iyyar adawar ya cika sosai, wannan ya jawo saura kiris Atiku ya zubar da hawayen farin ciki, ganin yadda aka tarbe shi da kyau.
Asali: Legit.ng