Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Abubakar, Ya Sauka a Ogun

Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Abubakar, Ya Sauka a Ogun

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP mai adawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya isa Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yau Laraba
  • Ana tsammanin tsohon mataimakin shugaban kasan zai gana da masu ruwa da tsaki na bangarorin rayuwa daban-daban
  • Gwamnoni irin su Aminu Tambuwal, Ademola Adeleke, Udom Emmanuel na cikin tawagar da suka isa wurin ganawar kafin Atiku

Ogun - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, ya dira Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ana sa ran tsohon mataimakin shugaban kasa wanda ke fatan gaje Buhari zai gana da masu ruwa da tsaki na bangare daban-daban a Abeokuta

Atiku a jihar Ogun.
Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Abubakar, Ya Sauka a Ogun Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Atiku ya isa birnin Abeokuta a jirgin sama da misalin karfe 1:57 na rana. Tun kafin zuwansa manyan kusoshin PDP na zaune suna jiransa a ɗakin taron da aka shirya.

Kara karanta wannan

Wike Ya Samu Tangarɗa, Gwamnan G-5 Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Yuwuwar Haɗewa da Atiku

Jiga-jigan da suka isa wurin taron sun hada da ɗan takarar gwanna a Ogun na PDP, Ladi Adebutu, abokin takararsa, Adekunle Akinlade, da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran wadanda aka hanga zaune kafin isowar Atiku sune, Gwamna Emmanuel Udom, na Akwa Ibom, Gwamna Ademola Adeleke na Osun da ɗan takarar gwamnan Legas a inuwar PDP, Abdul-Azeez Adediran.

Jiga-jigan PDP da ke tare da Atiku Abubakar

Haka zalika, tsohon mataimakin shugaban kasan ya isa wurin taron tare da rakiyar manyan kusoshin jam'iyyar PDP na ƙasa.

Wadanda ke tare za ɗan takarar kujera lamaba ɗaya a Najeriya sun hada da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Sauran jiga-jigan sun kunshi tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyintola, da kuma tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Liyel Imoke.

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari Inda Ya Samu Lambar Yabon Wanzar da Zaman Lafiya a Afrika

Bayan ganawa da masu ruwa da tsaki, Atiku zai halarci gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Ogun.

Na Kusa da Wike Ya Yi Magana Kan Sasantawa da Atiku

A wani labarin kuma Gwamnan tawagar G-5 mafi kusa da Wike ga bayyana kwarin guiwar shawo kan matsalar PDP gabanin zabe

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, yace jam'iyyar APC ba zata samu kofar lashe zabe ba bida haka yake son ganin zaman lafiya ya dawo a PDP.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya tal bayan Wike yace suna gab da cimma matsayar wanda zasu goyi bayan bayan raba gari da Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262