An Cigaba da Musayar Kalamai Tsakanin Bola Tinubu da Abokin Gabansa a APC
- Cacar baki ya gagara karewa tsakanin Tunde Bakare da kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu ba
- Fasto Tunde Bakare ya yi raddi ga Femi Fani Kayode wanda ya maida masa martani kan maganarsa
- Duk da ya ji kunya a zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa na APC, Bakare yana alfahari da kan shi
Lagos - Limamin cocin Citadel Global Community, Tunde Bakare, ya maida martani ga magoya bayan Bola Tinubu da suka yi masa raddi bayan kalamansa.
A rahoton da Vanguard ta fitar dazu, an ji cewa Fasto Tunde Bakare ya soki masu yi masa dariya saboda bai samu ko kuri’a daya a zaben tsaida gwanin APC ba.
Malamin addinin wanda ya zama ‘dan siyasa yake cewa ya tashi babu kuri’a ko daya a zaben fitar da gwani ne da takardun makarantan gaskiya, ba na bogi ba.
Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa
Bakare yake cewa mutuncinsa da kimarsa ba su zube ba saboda bai tabuka komai a zaben APC ba.
Ni ina da takardun gaskiya - Bakare ga APC PCC
Jaridar ta ce Bakare ya hakaito maganar da Michel De Montaigne ya taba yi, ya ce kowa ya san da zaman makarantun da ya yi karatu a gida da wajen Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Duk da bai yi nasara a zaben tsaida ‘dan takaran shugabancin Najeriya da jam’iyyar APC ta shirya a 2022 ba, Faston ya ce takardun karatun na sa abin alfahari ne.
An tasa Bola Tinubu a gaba
An dade ana zargin cewa akwai alamun ta-cewa a game da takardun karatun Bola Tinubu wanda ya doke Bakare da sauran mutane fiye da 10 wajen samun tikiti.
Tinubu yana ikirarin ya yi karatun sakandarensa da jami’a ne a garin Oyo da Birnin Chicago a Amurka, Sai dai hakan ya yi ta jawo alamar tambaya tun zaben 1999.
Abin da ya faru tsakanin Bakare da Tinubu
An samu rahoto Fasto Bakare ya yi wa mutane huduba da cewa su guji ‘emilokan’, wanda take ne da aka san ‘dan takaran shugaban kasar jam’iyyar APC da shi.
Bayan limamin na cocin Citadel Global Community ya yi wannan kira, sai kwamitin yakin neman zaben APC ya yi maza ya maida masa martani a makon nan.
Darektan harkokin sadarwa na zamani na kwamitin PCC, Cif Femi Fani-Kayode ya ce Bakare ba abin a kula ba ne domin ire-irensa ba su da wani nauyi a siyasa.
Bakare a martanin da ya yi, ya ce idan har bai da nauyi, meyasa za a shagala da yi masa raddi, ya jaddada cewa bai taba fadawa mabiyansa su zabi Tinubu ba.
Daily Trust ta rahoto 'dan takaran yana zargin Hadiman da yi wa Duniya karya.
Asali: Legit.ng