Atiku Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Yayin Da Tsohuwar Ministan Obasanjo Ta Tona Ƙarerayin Ɗan Takarar Na PDP

Atiku Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Yayin Da Tsohuwar Ministan Obasanjo Ta Tona Ƙarerayin Ɗan Takarar Na PDP

  • Tsohuwar minista karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo, Oby Ezekwesili, ta bukaci dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya dena karya
  • Yayin da ta ke mayar da martani kan ikirarin Atiku, Ezekwesili ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi karya da ya ce shine shugaban tawagar tattalin arziki karkashin gwamnatin Obasanjo
  • Atiku ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ya taka muhimmin rawa wurin tabbatar da cewa bangaren yan kasuwa suna aiki da kyau karkashin gwamnatin Obasanjo don shine shugaban tawagar tattalin arziki

Oby Ezekwesili, tsohuwar ministan ilimi a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta bukaci Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya dena yi wa mutane 'karya'.

Tsohuwar ministan ta furta hakan ne yayin martani kan ikirarin da tsohon shugaban kasar ya yi a shafinsa na Twitter na cewa shine ya jagoranci tawagar tattalin arziki karkashin gwamnatin Obasanjo.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Atiku da Oby
Atiku Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Yayin Da Tsohuwar Ministan Obasanjo Ta Tona Karerayin Dan Takarar Na PDP. Hoto: Atiku Abubakar, Oby Ezekwesili
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obi, wacce ta yi aiki a matsayin minista yayin da Atiku ke mataimakin shugaban kasa karkashin gwamnatin Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007, ta ce dan takarar na PDP bai taba zama shugaban tawagar tattalin arziki na Obasanjo ba wato (EMT).

Atiku, a shafinsa na Twitter a ranar Talata 17 ga watan Janairu, ya bayyana cewa shine shugaban tawagar tattalin arziki na gwamnatin Obasanjo.

Ya ce:

"A matsayi na na shugaban tawagar tattalin arziki, lokacin ina mataimakin shugaban kasa, na taka rawa sosai wurin tsara shirin farfado da bangaren yan kasuwa da neman a bawa masu saka hannun jari damar shigowa a dama da su wurin gina tattalin arziki. Kuma mun samu nasarori sosai."

Da ta ke martani kan ikirarin, tsohuwar ministan ta ce Atiku bai taba shugabancin tawagar kula da tattalin arziki ba a gwamnatin Obasanjo, tana mai kira ga dan takarar na shugaban kasa na PDP ya dena yaudarar mutane.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaba Buhari Yayin da Ya Isa Filin Taron Bikin Ranar Sojoji

Ta ce:

"Ya kai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, don Allah ta tambayi masu kula da shafinka na @Twitter su dena yi wa mutane karya. Ba ka taba shugabancin tawagar tattalin arziki ba.
"Wannan karyar mara amfani ba za ta zama maka alheri ba. Don Allah ka fada wa tawagar ka su dena."

Ga sakon a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164