Shugaba Buhari Ya Halarci Taron Bikin Ranar Sojoji, Bidiyo Ya Bayyana

Shugaba Buhari Ya Halarci Taron Bikin Ranar Sojoji, Bidiyo Ya Bayyana

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bikin ranar sojoji wanda ke gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu
  • Bikin ya samu halartan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da manyan jami'an gwamnati
  • Wannan shine bikin ranar soji na karshe da Buhari zai yi a matsayin shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojin kasa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin taron da ake gudanar da bikin ranar sojoji na shekarar 2023 a babban birnin tarayya Abuja.

Da isar shugaba Buhari filin taron da misalin karfe 10:05 na safe, sai aka isar da shi dandalin gaisuwa domin karrama shi ta hanyar sara masa.

Ranar sojoji
Shugaba Buhari Ya Halarci Taron Bikin Ranar Sojoji, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya kuma duba faretin jami’an tsaro karkashin jagorancin babban kwamandan birgade inda bayan nan ya ajiye furannin karrama jaruman da suka rasu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Tafka Asara, Gobara Ta Lakume Dukiyar Miliyoyin Naira a Babban Birnin Jiha

Wannan bikin karrama jaruman sojoji yan mazan jiya shine na karshe da Buhari zai yi a matsayin babban kwamandan rundunar soji, jaridar Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan tsaro da shugabannin sojoji.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Alkalin-alkalai na Najeriya, mambobin majalisar zartarwa ta tarayya, sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma'aikatan shugaban kasa, sakatarorin dindin da sauransu.

Bashir Ahmed ya saki bidiyon bikin

Har ila yau, hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya saki bidiyon taron wanda ke gudana a yau Lahadi, 15 ga watan Janairu a shafinsa na Twitter.

Kalli bidiyon a kasa:

Rundunar sojoji ta murkushe yan ta'adda sama da 50

A wani labarin, dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka yan ta'adda masu yawan gaske yayin da suke ci gaba da yakar ta'addanci da fatattakar miyagu daga yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban Kasa Buhari Ya Gana da Wani Dan Takara, Ya Daga Masa Hannu a Aso Rock

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta bayyana, dakarunta sun murkushe mayakan ISWAP da na Boko Haram fiye da 50 a wani samame da suka kai masu ta sama da kama tsakanin ranar 25 ga watan Disamba zuwa 12 ga watan Janairu.

Hakazalika, wasu yan ta'adda da iyalansu sun mika wuya ga rundunar inda tuni aka mika su ga hukumomin da suka dace don daukar mataki na gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel