Sabon Matsala Ta Bullo A PDP Yayin Da Buhari Ta Yi Babban Zargi Kan Ayu

Sabon Matsala Ta Bullo A PDP Yayin Da Buhari Ta Yi Babban Zargi Kan Ayu

  • An zargi shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, da kara ingiza wutar rashin jituwa a jam'iyyar PDP ta Kano
  • Lailah Buhari, yar takarar sanata na Kano Central, ce ta zargi Ayu yayin da ta ke bayyana tsoron cewa rashin jituwa a jam'iyyar zai iya janyo su fadi zaben watan Fabrairu
  • Buhari, wacce a baya-bayan nan kotun daukaka kara ta jadada nasarta, ita ce yar takara mace daya kawai da ke takara a dukkan jihar Kano a 2023

Kano, Kano - Lailah Buhari, yar takarar jam'iyyar PDP na Kano Central, ta zargi kwamitin ayyuka (NWC) na babban jam'iyyar hammayar ta ingiza wutar rikicin cikin gida a jam'iyyar a jihar.

Buhari, ta ware shugaban jam'iyyar na kasa Iyorchia Ayu ta zargi shi ta ingiza wutar rabuwar kai tsakanin kungiyoyin da ke jam'iyyar yayin da ta ke bayyana damuwa cewa hakan na iya shafar nasarar jam'iyyar a zabe mai zuwa a Fabrairu, Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Laila Buhari
Sabon Matsala Ta Bullo A PDP Yayin Da Buhari Ta Yi Zargi Mai Karfi Ga Ayu. Hoto: Laila Buhari
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da Buhari ta ce game da Ayu kan PDP na Kano

Yar siyasar wacce ita ce kadai yar takara mace a dukkan jam'iyyun siyasa na Kano a zaben 2023 ta furta hakan ne yayin magana da ta yi da manema labarai kan niyyarta na kafa tarihi a zaben 2023.

A baya-bayan nan, kotun daukaka kara ta jadada sahihancin zaben cikin gida da ta samar da Buhari kan wacce dayan bangaren suka yi ta Nuru Danburam ya yi nasara.

An zabi Buhari ne zaben cikin gida karshen shugabancin Shehu Sagagi, shugaban bangare na PDP yayin da an zabi Danburam a wani zaben da aka yi karkashin bangaren Aminu Wali.

Abin da ke faruwa game da Buhari, PDP, Iyorchia Ayu, Kano, Zaben 2023

Da farko, Danburam ya samu nasara a babban kotun tarayya amma kotun daukaka kara ta soke hukuncin ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta amince da takarar Buhari.

Kara karanta wannan

Ba ni ba APC: Shugabar matan jam'iyyar ta sauya sheka, ta jikawa wani gwamna aiki

A halin yanzu, Danburum yana kotun tarayya don kallubalantar hukuncin da kotun daukaka karar, amma Buhari ta bayyana kwarin gwiwar cewa za ta yi nasara.

Rikicin PDP: Nyesom Wike ya bayyana dabarar cin zaben 2023 a Jihar Ribas

Kun ji cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom ya ce jam'iyyar Peoples Democratic Party, wato PDP ce za ta lashe zabe a jihar a zaben 2023.

Amma ya ce ba dole ne Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya yi nasara ba a jihar har fa sai an cika sharrudan da ya bada, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel