Rikicin PDP: Wike Ya Bayyana Dabarar Cin Zaɓen 2023 A Jihar Rivers, Ya Ba Atiku Sabon Sharaɗi

Rikicin PDP: Wike Ya Bayyana Dabarar Cin Zaɓen 2023 A Jihar Rivers, Ya Ba Atiku Sabon Sharaɗi

  • Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bugi kirji yana cewa PDP za ta ci zabukan jihar, ciki har da na gwamna da majalissu
  • Wike, amma, ya bayyana rashin tabbas game da samun nasarar jam'iyyar a zaben shugaban kasa
  • Gwamnan, cikin wani sako mai dauke da boyayyen sako, ya ce dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ba zai ci jihar ba idan ba a yi abin da ya dace ba

Port Harcourt, Rivers - Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers, ya ce jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, za ta ci zabe a jiharsa a 2023.

Amma, gwamnan ya ware zaben shugaban kasa ya kore yiwuwar nasarar Atiku Abubakar a jihar, sai dai idan ya yi abin da ya dace, Vanguard ta rahoto.

Wike da Atiku
Rikicin PDP: Wike Ya Bayyana Dabarar Cin Zaɓen 2023 A Jihar Rivers, Ya Ba Atiku Sabon Sharaɗi. Hoto: Photo Credit: Nyesom Wike, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Wike ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sabbin ofisoshin sadarwa a gunduma 319 da mazabu 32 a Port Harcourt, babban birnin jihar.

Karin bayani kan rikicin Atiku, Wike da PDP

Gwamnan ya kuma soki tsohon ministan sufuri, Abiye Sekibo, ya bayyana shi a matsayin dan siyasa wanda bai da hurumi ya yi magana a madadin jihar Rivers.

Wike ya ce tsohon ministan ya yi ikirarin cewa Wike yana da alaka na kusanci da jihar Rivers kuma jihar da amfana da shi yayin da ya ke mataimakin shugaban kasa.

Gwamnan na PDP ya jadada cewa Sekibo yana da alaka ta kusanci da Atiku amma ba jihar Rivers ba.

Wanene zai yi wa Atiku kamfen a Rivers

Gwamnan ya kuma tunatar da cewa Sekibo ne ministan sufuri a lokacin da Atiku ke mataimakin shugaban kasa, ya yi tambayar cewa idan mutane za su iya nuna wani aiki da ya yi a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Gama Ragargazar Shugaban PDP, Gwamna Wike Ya Dura Kan Jagoran Jam’iyya

Wani sashi na jawabinsa ya ce:

"PDP za ta ci zabe a jihar mu. Bana boye hakan idan aka batun zaben gwamna, majalisar tarayya, sanata da majalisun jihohi. Daya zaben (shugaban kasa) ba mu yanke shawara ba, har sai an yi abin da ya dace."

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Mr Nyesom Wike na Jihar Rivers.

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel