Kuri'a Daya Tak Wike Yake da Ita, Mu Mun Ci Gaba, Hadimin Atiku
- Hadimin Atiku Abubakar, 'dan takarar shugaban kasa a PDP, Phrank Shaibu, yace sun cigaba da kamfen duk da babu Gwamna Wike na jihar Ribas
- Yace Gwamna Wike da sauran mukarabbansa duk kuri'u daddaya gare su kuma ko da babu su sun cigaba da lamurransa don tukarar zabe
- Ya sanar da cewa, Atiku bashi da wata kebantacciyar matsala da Wike duk da yana cewa sun kusa rufe tagar sasanci, su zasu bi ta kofa a sasanta
Phrank Shaibu, mataimaki na musamman kan sadarwar jama'a na 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yace Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ba shi da wani tasiri a zaben shugaban kasa da ke gabatowa.
Shaibu, yayin zantawa da Channels TV a shirin Sunday Politics, yace Wike kuri'a daya tak ya ke da ita a zaben shugabancin kasa.
Wike, shugaban gwamnonin G-5 wadanda suka fusata da yadda jam'iyyar PDP ke gudanar da lamurranta, a makon da ya gabata yace suna dab da rufe tagar sasanci.
Tuntuni gwamnonin G-5 din suke ta gina alaka mai karfi da 'dan takarar shugaban kasa na APC, Ahmed Bola Tinubu da kuma na LP, Peter Obi, duk da har yanzu suna jam'iyyar PDP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, yayin zantawa a shirin, Shaibu yace Atiku ba shi da wata kebantacciyar matsala da Wike inda ya jaddada cewa yayin da ake cigaba da neman sasanci, Atiku ya cigaba da kamfen dinsa don zaben watan Fabrairu.
Yace:
"Abun dadin shi ne kamfen din mu na ci gaba. Mun ce da farko don Najeriya ne, ba don PDP kawai ba.
"Atiku Abubakar ba shi da wata kebantacciyar matsala da Wike. Sa'o'i kadan da suka gabat na karanta a jarida cewa ya ce sun kusa rufe kofar sasanci da PDP."
“Za ka iya rufe tagar amma kofar bude ta ke saboda 'dan takarata Atiku Abubakar, ba 'dan ta'adda bane. Don haka ba sai ya bi ta taga ba, zai shigo ta kofa.
"Matsalar ita ce PDP wani gida ne babba. Ba wai don Gwamna Wike ba. Wike gwamna ne daya tak kuma mamba daya tak kuma kuri'a daya gare shi, haka sauran gwamnonin hudu da suke mambobin G-5.
“Toh, muna kallon yadda lamarin ya ke ta yadda za mu taho tare idan sun shigar jirginmu. Saboda jirginmu tafiya ya ke kuma yana tafe da kyau, ko ana gobe zabe ne, ko ana saura wata, ko sauran kwanaki, duk daya ne."
- Ya kara da cewa.
Jam'iyyar APC ta bukaci ICPC da EFCC da ta damke Atiku Abubakar
A wani na daban, jam'iyyar APC ta bukaci hukumar yaki da rashawa ta EFCC da ta ICPC da su kama Atiku Abubakar, 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.
Hakan ya fallasu ne a wata wasika da Fetsu Keyamo ya aikewa EFCC wacce yace sun yi dogaro ne da ikirari da zargin da tsohon hadimin Atiku Abubakar, Michael Achimugu yafitar.
Asali: Legit.ng