Asiri Ya Tonu: Yadda ‘Yaradua Ya Zama Shugaban Najeriya a Maimakon IBB a 2007

Asiri Ya Tonu: Yadda ‘Yaradua Ya Zama Shugaban Najeriya a Maimakon IBB a 2007

  • Kassim Afegbua ya ce Ibrahim Badamasi Babangida aka tsara zai karbi mulki a hannun Olusegun Obasanjo
  • Da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ki goyon bayan Obasanjo ya zarce, sai aka samu matsala a tsakaninsu
  • Shugaba Obasanjo ya dauko Gwamna Umaru Yar’adua, wanda shi IBB ya so ya zama masa DG a wajen kamfe

Abuja - Kassim Afegbua wanda ya rike Kwamishinan yada labarai a Edo, ya ce an tsara yadda Ibrahim Badamasi Babangida zai gaji Olusegun Obasanjo.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto dazu, da farko an yi niyya Umaru Yar’adua ne zai zama shugaban kwamitin yakin neman zaben Ibrahim Babangida.

Kassim Afegbua ya ce inda aka samu matsala shi ne da Janar Ibrahim Babangida ya hana Shugaba Obasanjo neman tazarce na biyu a wani taro a fadar Aso Rock.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Emilokan Ba Musulmin Kwarai Bane - Melaye Ya Doke Tinubu a Gasar Karanta Fatiha

A wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, Afegbua ya ce Obasanjo ya kira taro da tsofaffin shugaban kasa, sai suka ki goyon bayan yunkurinsa na zarcewa a ofis.

Babangida ya fusata Shugaban kasa

A wajen Babangida ne ya nuna adawarsa, a dalilin haka Afegbua ya ce shugaban kasar ya yake shi, ya dauko Yar’adua yana gwamna, ya zama magajinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin da Obasanjo bai sani bas hi ne, Yar’adua aka so ya zama DG a kwamitin zaben Babangida.

‘Yaradua
‘Yaradua Ya Zama Shugaban kasa a Mayun 2007 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Afegbua ya maidawa Obasanjo amsa

‘Dan siyasar yake cewa yunkurin Cif Olusegun Obasanjo na cigaba da mulki bayan cikar wa’adinsa a 2007 ba wani boyayyan abu ba ne, a zahiri abin yake.

An rahoto Afegbua yana maidawa tsohon shugaban na Najeriya martani cewa ya nemi sake zarcewa a kan mulki, amma bai yi nasara wajen hakan ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Jega Da AbdulAziz Matsayin Masu Magana Da Yawunsa Na Arewa

A cewar tsohon Kwamishinan, a lokacin Obasanjo bai iya samun goyon bayan Gwamnoni, ‘yan jarida da sauran wadanda suka taimaka masa 1999 ba.

A jawabinsa, tsohon marubucin ya bada labarin yadda aka taso shi a gaba a karshen gwamnatin Obasanjo, yana zargin cewa ana neman a hallaka shi a Abuja.

A ranar 23 ga watan Agustan 2006, Afegbua yace an nemi a kashe shi, kafin nan kuwa ya ce sai da aka ja-kunnen shi a kan irin rubuce-rubucen da yake yi.

A Satumban 2006 aka shirya Emmanuel Iwuayanwu zai halarci taron Ibo Amurka, a nan ne Afegbua yace aka so a tallata batun tazarcen, amma ya gaza.

Idan maganarsa gaskiya ne, an nemi a jawo Sarakuna da manyan jami’an gwamnati, kuma aka rabawa ‘yan majalisa kudi saboda Obasanjo ya zarce a mulki.

Ban nemi karin tazarce ba - OBJ

An samu labari Cif Obasanjo wanda ya yi mulki a lokacin soja da kuma farar hula, yayi karin haske a kan zargin bankara tsarin mulki domin ya yi ta mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Osun Ya Fadi Abin da Za a Rika Tuna Buhari da Shi Bayan Mayun 2023

A hirar da aka yi da shi, Obasanjo ya ce ba zai rika bin Peter Obi zuwa yawon kamfe ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng