APC Ta Dakatar Da Gangamin Kamfen Dinta Don Alhinin Mutuwar Mambobin PDP da Suka Mutu a Hatsarin Mota

APC Ta Dakatar Da Gangamin Kamfen Dinta Don Alhinin Mutuwar Mambobin PDP da Suka Mutu a Hatsarin Mota

  • Jam'iyyar APC a jihar Filato ta dakatar da harkokin kamfen dinta na kwanaki uku don jimamin mambobin PDP da suka mutu a hatsarin mota
  • Mummunan hatsarin mota ya cika da mambobin jam'iyyar PDP a hanyarsu ta dawowa daga wajen kamfen inda wasu suka kwanta dama, wasu sun ji munanan rauni
  • Dan takarar PDP a jihar, Nentawe Yilwatda, ma ya dakatar da harkokin kamfen dinsa don juyayin rashin da suka yi

Plateau - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar Filato ta dakatar da gangamin yakin neman zabenta na tsawon kwanaki uku don karrama wasu magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka mutu a hatsarin mota.

Jaridar The Cable ta rahoto cewan magoya bayan PDP 16 sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyarsu ta dawowa daga gangamin kamfen din jam'iyyar wanda ya gudana a yankin Pankshin da ke jihar.

Kara karanta wannan

Da Gaske ICPC Ta Kama Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Kan Badakalar Biliyan N12? Aliyu Sokoto Ya Fayyace Gaskiyar Lamari

Jihar Filato
APC Ta Dakatar Da Gangamin Kamfen Dinta Don Alhinin Mutuwar Mambobin PDP da Suka Mutu a Hatsarin Mota Hoto: Punch
Asali: UGC

A wata sanarwa da ya fitar, Nentawe Yilwatda, dan takarar gwamnan APC a Filato ya ce ya dakatar da gangamin kamfen din ne don ba shi da mambobin jam'iyyarsa damar taya PDP da yan uwan mamatan alhinin rashin da suka yi.

Dan takarar na APC wanda ya samu rakiyar mambobin kwamitin yakin neman zabensa ya kuma ziyarci wadanda abun ya ritsa da su a asibitin koyarwa na jami'ar Jos.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya mika ta'aziyyarsa ga yan uwan wadanda suka rasu a hatsarin sannan ya yi addu'a kan Allah ya kiyaye gaba.

Dan takarar gwamnan PDP a Filato ya tsayar da harkokin kamfen dinsa

A wani lamari makamancin wannan, Caleb Mutfwang, dan takarar gwamnan PDP a jihar, shi ma ya dakatar da harkokin kamfen dinsa don alhinin mutuwar mamatan.

Yiljap Abraham, daraktan labaran kwamitin yakin neman zaben Atiku-Mutfwang ya sanar da ci gaban, yana mai cewa dukkanin wadanda suka jikkata sun farfado kuma cewa suna samun sauki.

Kara karanta wannan

Zan Bayar Da Ilimi Kyauta Idan Na Zama Gwamnan Kano - Abba Gida-gida

Ya ce marasa lafiya 64 na nan suna samu kulawar likitoci a asibitoci mabanbanta.

Abraham ya ce JUTH na kula da mutum 24, asibitin Nisi Domino 20, asibitin Infinity takwas, asibitin Cottage hudu sannan asibiyin Panyam mutum takwas, rahoton The Guardian.

A wani labari na daban, dan takarar jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin bayar da ilimi kyauta ga yan asalin jahar Kano idan ya zama gwamna a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel