Kano 2023: Zan Yaki Cin Hanci Da Rashawa Don Bayar Da Ilimi Kyauta, Abba Kabir Yusuf

Kano 2023: Zan Yaki Cin Hanci Da Rashawa Don Bayar Da Ilimi Kyauta, Abba Kabir Yusuf

  • Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar su Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf ya ce zai bayar da ilimi kyauta idan ya lashe zabe
  • Abba Gida-gida ya ce zai cimma wannan kudiri nasa ne ta hanyar dakile cin hanci da rashawa a jihar
  • Ya kuma bayyana tanadi na musamman da ya yi wa matasa don tallafawa rayuwarsu

Kano - Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a inuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa idan har aka zabe shi a zaben 2023, gwamnatinsa za a mayar da hankali wajen bayar da ilimi kyauta ga asalin yan Kano.

Dan takarar wanda ake yiwa lakabi da Abba gida-gida ya bayyana hakan ne a yayin muhawarar masu neman kujerar shugabancin Kano wanda sashin Hausa na BBC ta shirya a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Abba da jigon tafiyar Kwankwasiya
Kano 2023: Zan Yaki Cin Hanci Da Rashawa Don Bayar Da Ilimi Kyauta, Abba Kabir Yusuf Hoto: @Kyusufabba
Asali: UGC

Da aka tambaye shi kan inda zai samu wannan kudi na bayar da ilimi kyauta a jihar alhalin ana fama da koma bayan tattalin arziki, Abba ya ce:

''Idan ka toshe kafar wawure kudaden jama'a a Kano to ka yi maganin matsalar''.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana cewa zai habbaka hanyoyin samun kudaden shiga ta hanyar nemo tallafi a wajen kungiyoyin bayar da tallafi domin tallafa wa ilimi a jihar.

Har ila yau, dan takarar ya ce zai bayar da muhimmanci wajen daukar isassun malaman makaranta domin wadata jihar da malamai.

Za mu farfado da makarantu 26 don koyawa matasa sana'o'i

Har ila yau, dan takarar ya ce akwai babban tanadi da ya yiwa matasa inda ya ce musamman sun kirkiro wasu makarantu 26 da basa aiki sun farfado da su don tallafawa matasa a koya masu sana'o'i.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamna a 2023 Ya Yi Alƙawarin Kafa Gwamnati Bisa Koyi da Annabi Muhammad SAW

Ya ce:

"Akwai magana ta matasa wanda dama takenmu kenan 'ina matasa'·
"Matasa su sani cewa muna da abubuwa masumman mun kirkiro makarantu 26 wadanda basa aiki yanzu za mu farfado da su za mu koyawa matasa sana'o'i·"

Za mu yi biyayya ga duk wanda Allah ya nufa da zama gwamnan Kano, Gawuna

Mun ji a baya cewa dan takarar gwamnan Kano a APC, Nasiru Gawuna ya ce za su yi mubaya'a ga duk wanda Allah ya bai wa mulkin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel