Sabbin Zuwa Sun Kwace Jam’iyyar: Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar

Sabbin Zuwa Sun Kwace Jam’iyyar: Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Ebonyi, Dr Paul Okorie
  • Okorie, tsohon kwamishinan ayyuka, sufuri da gidaje ya yi murabus daga jam'iyyar yan makonni kafin babban zaben 2023
  • Tsohon jigon na APC wanda ya fito daga Mgbom Ward 3 (Okposi) a karamar hukumar Ohaozara ya bayyana dalilinsa na barin jam'iyyar

Jihar Ebonyi - Dr Paul Okorie, babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya fice daga jam'iyyar mai mulki gabannin babban zaben 2023.

Okorie wanda ya fito daga Mgbom Ward 3 (Okposi) a karamar hukumar Ohaozara ya yi murabus daga matsayin dan jam'iyya a wata wasika mai kwanan wata Talata, 3 ga watan Janairu 2023.

Okorie da wasikar ficewarsa daga APC
Sabbin Zuwa Sun Kwace Jam’iyyar: Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar Hoto: Nwele Ilodibe, Amb Martins Chinonso Nwede
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ya aika wasikar ga shugaban jam'iyyarsa a gudunmarsa.

Kara karanta wannan

Makonni Gabanin Babban Zabe, Babban Jigon APC Kuma Tsohon Kwamishina Ya Bar Tsagin Tinubu

Dalilin da yasa Okorie ya bar APC

Okorie, wanda ya taba rike mukamin kwamishinan ayyuka, sufuri da gidaje, ya zargi tsohuwar jam'iyyarsa ta APC da rashin nuna muhimmanci ga abubuwa da kuma rashin jajircewa a aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce shugabancin APC a matakin kasa ta bari sabbin mambobi a Ebonyi sun kwace ragamar jam'iyyar yayin da aka bar tsoffin mambobi a rashin tabbass, rahoton Within Nigeria.

Wani bangare na wasikar na cewa:

"Duk da jajircewa da kokarinmu, shugabancin APC na kasa ya taimakawa sabbin shiga jam'iyyar sun kwace ragamar abubuwa a Ebonyi inda suka bar tsoffin mambobi a wani hali da rashin madafa.
"Da wannan dalili na sama ne nake cewa sai wata-rana ga jam'iyyar All Progressives Congress kuma ina yi wa jam'iyyar fatan alkhairi."

An yi wa APC mai kankat, mambobin jam'iyyar sama da 20,000 sun fice zuwa PDP a Bauchi

Kara karanta wannan

2023: Hantar PDP, Atiku Ta Kada Yayin Da Yar Tinubu Ta Ziyarci Babban Dattijon Arewa, Bayanai, Hotuna Sun Fito

A wani labarin, yayin da babban zaben 2023 ke kara gabatowa, jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rasa dubban mambobinta a jihar Bauchi inda suka koma babbar jam'iyyar adawar kasar wato PDP.

Kamar yadda masu sauya shekar suka bayyana, sun koma tafiyar PDP ne saboda tarin nasarorin da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya samu a jihar musamman ma a bangaren samar da ababen more rayuwa ga al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel